1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya za ta inganta dangantaka da Afirka

Yusuf Bala Nayaya
December 24, 2017

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya tafi kasar Sudan a wannan rana ta Lahadi a ziyarar da ya tsara ta kwanaki biyu da zai fara da kasar Sudan, sannan ya tafi Chadi da Tunisiya.

https://p.dw.com/p/2ptxH
Afrikareise Erdogan in Mosambik
Erdogan da mai dakinsa a ziyara zuwa MozambikHoto: picture-alliance/AP Photo/K. Ozer

Erdogan ya fadawa taron manema labarai a birnin Ankara cewa ya dauki sake inganta dangantaka da kasashen Afirka da muhimmancin gaske, kuma Turkiya na son bude ofishin jakadancinta a dukkanin kasashen Afirka.

Ya kuma yi jinjina da godiya ga Shugaba Omar al-Bashir na Sudan din saboda halartarsa taron koli da aka yi a Istanbul kan Birnin Kudus bayan da Shugaba Donald Trump ya bayyana birnin a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Shi dai Shugaba Al-Bashir na da sammacin kasa da kasa a kansa a kotun da ke hukuntan masu manyan laifuka ta ICC saboda zargin kisan kiyashi da haddasa yaki a Sudan.

A lokuta da dama dai Erdogan ya sha kira ga kasashen na Afirka su rufe makarantu da ke karkashin Fethullah Gulen, malamin addinin Islama nan da ke zaune a Amirka saboda zarginsa da hannu a yunkurin kifar da gwamnatinsa.