1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta janye zargin da take wa kamfanonin Jamus

Abdul-raheem Hassan
July 24, 2017

Ma'aikatar cikin gidan Jamus ta ce hukumomin Turkiyya sun janye bukatar neman bayanan sirri a kan wasu kamfanonin kasar Jamus da take zargin su da tallafa wa aiyukan ta'adanci.

https://p.dw.com/p/2h3xN
Deutschland Innenministerkonferenz in Dresden
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Kahnert

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya ce ya samu tabbacin wannan mataki da Turkiyya ta dauka ta wayar tarho da suka yi da ministan cikin gidan kasar Turkiyya Suleyman Soylu. A yanzu dai Turkiyya ta bada tabbacin janye batun zargin kamfanonin na Jamus daga 'yan sandan cikin gida da ke shirin gudanar da binciken.

Dama dai matsin lambar da Turkiyya ke wa ma'aikatar shari'a da hukumar 'yan sandan cikin gida a Jamus, na cikin manyan batutuwan da ke dada tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu. Ko da yake akwai batun rufe wani dan jarida kuma dan fafutukar kasar Jamus din da mahukuntar Turkiyya suka yi a baya-bayannan bisa zargin alaka da ta'addanci.