1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Twitter ta dade shafin shugaban Najeriya

June 2, 2021

Twitter ta dakatar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari daga amfani da shafinsa har na tsawon sa'oi goma sha biyu.

https://p.dw.com/p/3uN5E
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Kamfanin kafar sadarwa na Twitter ya janye wani sako da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya wallafa a shafinsa tare da dakatar da shi daga amfani da shafin na tsawon sa'oi goma sha biyu sakamakon wani sakon barazana da ya wallafa.

Shugaban dai ya mayar da martani ne dangane da hare-haren da masu rajin kafa kasar Biafara suka zafafa kaiwa a kan gine-ginen gwamnatin musamman ofisoshin jami'an tsaro da na hukumar zabe.

Kafar ta Twitter ta ce kalaman shugaban na haska hotunan irin abin da ya taba faruwa a kasar na yakin basasar a shekarun 1967 zuwa 1970 inda mutane sama da miliyan guda suka rasa rayukkansu mafi akasari mata da yara kanana.