1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Umarnin kame daruruwan sojoji a Turkiyya

Mohammad Nasiru Awal ATB
November 29, 2017

Wannan matakin da aka dauka a birnin Santambul, ya shafi sojojin kasar da ke zargi suna da alaka da Fethullah Gülen.

https://p.dw.com/p/2oUzl
Türkei Putschisten werden festgenommen
Hoto: picture-alliance/AA/E. Payan

A kasar Turkiyya an sake ba da umarnin kame daruruwan sojojin kasar da ake zargi magoya bayan fitaccen malamin kasar ne Fethullah Gülen. Wannan matakin da aka dauka a birnin Santambul, an mayar da hankali kan sojojin kasar, inji kamfanin dillancin labarun Turkiyya Anadolu. A jimilce ma'aikatar shari'ar Turkiyya ta ba da sammacin kame sojoji 360.

Shi dai babban malamin Fethullah Gülen da ke zaune a kasar Amirka, ana zarginsa da kulla makarkashiyar wani yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara. Sai dai ya sha musanta wannan zargi.

Tun bayan yunkurin juyin mulki a watan Yulin shekarar 2016, an kame akalla mutane fiye da dubu 50 a kasar ta Turkiyya bisa zargin alaka da Gülen. An sako mutane dubu 150 da suka hada da jami'an soji da ma'aikatan gwamnati da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.