1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNDP: Talauci ya assasa tsatsauran ra’ayi

Zainab Mohammed Abubakar RGB
September 13, 2017

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP ta gabatar da wani rahoton bincike a kan karuwar matsanancin ra'ayi, sakamakon da ke danganta wannan akida da talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

https://p.dw.com/p/2juNE
United Nations Development Programme (UNDP) Hauptquartier in Gaza-Stadt
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/A. Amra

Sakamakon Rahoton Hukumar ya ci gaba da nunar da cewar akidar masu tsananin ra'ayin ba shi da wata nasaba da addini face talauci da takaicin rayuwa da kuma matsalar rashin aikin yi, rahoton ya yi dogaro da tambayoyin da hukumar raya kasashe ta gudanar inda ta dauki tsawon shekaru biyu tana yi wa tsoffin 'yan kungiyoyin ta'addancin wajen 500 a sassa daban daban a nahiyar Afirka.Tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2016 a cewar rahoton, aika aikan 'yan ta'adda ya ritsa da mutane da yawansu ya kai dubu 33. Najeriya daya ce daga kasashe masu yawa a nahiyar Afirka da suka tsinci kansu cikin yanayi na kakanikayi wajen yaki da ayyukan tarzoma.

Bayan Boko Haram da ke fafutuka a yankin arewa maso gabashin kasar, tsawon shekaru kenan mayakan Al-Shabaab ke tabka ta su ta'assar a Somaliya, kana Mali tana fama da rassan mayakan al-Ka'ida. Khadija Hawaja Gambo da ke fafutukar kare hakkin jama'a a Najeriya ta jima ta na nazarin dalilin da ya sa yankin arewa maso gabashin kasar kadai ke fama da matsalar boko Haram ta kuma yi  nazarin rahoton Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar mai shafuka 128, ta na mai ra'ayin cewar duk wanda ya san addinin Musulunci, ya san cewar akidar mayakan Boko Haram da ke fakewa da addinin Islama yaudara ce kawai, domin babu abin da ya danganta akidunsu da Musulunci.

Kwararru a fannin sanin halayyar dan Adam da masu fafutuka suna da yakinin cewar, akasarin wadanda ke shiga irin wadannan kungioyoyi mutane da suka riga suka rasa mafita dangane da halin da suke ciki na kuncin rayuwa.