1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Mutuwar jarirai ta karu a kasashe matalauta

Abdullahi Tanko Bala
February 20, 2018

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya koka akan yadda talauci da ringimu ke ci gaba da yin sanadiyyar mutuwar jarirai.

https://p.dw.com/p/2t12F
Jemen Sanaa Unterernährte Kinder
Hoto: picture alliance/Photoshot/M. Mohammed

Babu dai wata kasa a nahiyar Afirka da rahotan na UNICEF ya sa a cikin jerin kasashen da ake samun ci gaba wurin kiyaye mutuwar jarirai. Alkaluma sun nuna cewa akwai jan aiki a gaban kasashe irinsu Pakistan da Chadi da Sudan ta Kudu da Mali da kuma wasu kasashe guda biyar, wadanda galibinsu na Afrika ne. To ko me hakan ke nufi ga lafiyar jarirai a kasashen Afrika? Alain Prual shi ne ke kula da ofishin UNICEF shiyyar da Dakar na kasar Senegal.

Somalia Flüchtlingslager in Doolow
Hoto: picture-alliance/Zumapress/S. Ruibo

Lallai akwai bukatar gwamnatocin Afrika su kara kason kudin da suke kashewa a bangarori daban daban domin samar da lafiya ga jarirai. Mu dai a UNICEF za mu ci gaba da taimaka musu da bayanai da shawarwari akan yadda za su bada kulawar da ta dace wajen rage mace-macen jariran. "

Rahaton dai ya nuna cewa, a duk shekara,  jarirai 2,600,000 ke mutuwa a watanin na farko bayan haihuwarsu.  A kowace rana kuma jarirai 7000 ne ke mutuwa a duniya.  Galibi mutuwar jariran tafi kamari a kasashen Pakistan da Chadi da sauran kasashe inda  talauci da rikici da kuma rashin ingantaccen tsari, suka yi "katutu". Sai dai a lokuta da dama shugabanni kan ce su na iyakar kokarinsu. Amma kuma Alain Prual yace, su ma basu ce shugabanni ba sa kokari ba sai dai ya kamata su kara dage damtse.

Süd-Sudan Mütter und Kinder beim UNICEF-Gesundheitszentrum in Nimini village
Hoto: Reuters/S. Modola

Rage mace-macen kananan yara lallai abu ne da gwamnatoci suka sa a gabansu. Amma ya kamata mu sani akwai wasu abubuwa da kan dauke musu hankali, saboda ko a bangaren lafiya har yanzu akwai cututtuka irinsu Pneumonia da ke bukatar  kulawar gwamnati. Dalili ke nan da yasa har yanzu gwamnatoci ba su magance mutuwar jarirai yadda ya kamata ba"

Kasar Japan ita ce tazo ta daya a jerin kasashe goma sha biyu da UNICEF ta ce jarirai ke da sukunin rayuwa. Yayin da, asusun, ya bayyana wasu kasashen a matsayin na karshe wurin kare mutuwar jarirai. 

Akasarin kasashen Afrika basu da wadatattun kuma kwarrarun jami'an kiwon lafiya. A wuraren da ake dasu kuma, sai ka ga an kai su inda bai dace ba. "

A yanzu dai shawarar da asusun UNICEF ya bayar ita ce, gwamnatoci su tashi tsaye wurin samar da wadattatun ungozoma da tsaftataccen ruwan sha da sabulai. Kuma iyaye su bai wa jaririnsu nonon a cikin awa daya da haihuwarsu, sannan a ci gaba da ba da ingantaccen abinci da kuma kulawa.