1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Venezuela: Kotu ta yi watsi da karar Lopez

Zainab Mohammed AbubakarAugust 13, 2016

Wata kotu a kasar Venezuela ta yi fatali da daukaka karar da shugaban adawa Leopoldo Lopez ya shigar gabanta, dangane da hukuncin daurin shekaru 14 da aka yanke masa

https://p.dw.com/p/1Jhjw
Venezuela Leopoldo Lopez
Hoto: Getty Images/AFP/J. Barreto

Hukuncin daurin shekaru 14 da aka yanke masa dai ya biyo bayan irin rawar da ya taka nena boren adawa da gwamnati shekaru biyun da suka shige.

Lopez ya yi fice a tsakanin 'yan adawa masu mara masa baya, saboda yadda yake zargin shugaba Nicholas Maduro na Venezuelan da take hakkin bil adama.

Amurka da Majalisar Dunkin Duniya da wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a na kasa da kasa dai, sun yi kira da a saki Lopez.

Hukuncin da aka yankewa shugaban adawan a bara, ya lalata 'yar kwarya-kwaryar danganta na 'yan watanni da ya fara farfadowa tsakanin Washinton da Caracas.

Hukuncin dai ya zo ne, watanni kalilan bayan kaddamar da tattaunawar maido da huldodi tsakanin Amurka da Venezuela, bayan sun kwashe sama da shekaru 10 basa dasawa.