1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilan manyan kasashe sun bijire wa taron Saudiyya

October 18, 2018

Ministocin Birtaniya da Faransa da na Holland, sun sanar da janyewa daga halartar babban taron harkokin saka jari da za a yi a Saudiyya.

https://p.dw.com/p/36nTK
Riad Treffen GCC Außenminister
Hoto: Getty Images/AFP/F. Nureldine

Manyan ministocin kasashen Birtaniya da Faransa da na Holland, sun sanar da janyewarsu daga halartar babban taron nan kan harkokin saka jari da za a yi a Saudiyya a makon gobe, saboda damuwa kan bacewar dan jaridar nan dan Saudiyya, Jamal Khashoggi.

Shi ma sakataren baitul malin Amirka, Steven Mnuchin, ya bayyana janyewarsa daga halartar taron, dai dai kuma lokacin da Shugaba Donald Trump ke kaffa-kaffa da batun, saboda kawancen Amirka da Saudiyya.

Amirkar dai kamar Birtaniya da kuma Faransa, manyan kasashe ne da ke sayar da makamansu ga Saudiyya.

A halin da ake ciki ma dai Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo, ya shaida wa Shugaba Trump cewa akwai bukatar bai wa Saudiyyar lokaci don ta kammala bincikenta kan batun na Khashoggi,

Mr. Pompeo, ya ziyarci Saudiyya da ma Turkiyya dangane da batun.