1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani dan takara ya janye daga zaben Côte d'Ivoire

Gazali Abdou tasawaOctober 23, 2015

Charles Konan Bani tsohon firaministan Cote d'Ivoire ya janye takararsa daga zaben shugaban kasa na ranar Lahadi mai zuwa a bisa zargin rashin adalci cikin tsarin zaben

https://p.dw.com/p/1GtRv
Elfenbeinküste Kommunalwahlen
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A Côte d'Ivoire tsohon firaministan kasar Charles Konan Bany ya bada sanarwar a wannan Jumma'ar cewar ya janye takararsa daga zaben shugaban kasar da ake shirin gudanarwa a ranar Lahadi mai zuwa.

Lokacin wani taron manema labarai da ya kira, Charles Konan Bani wanda yake daya daga cikin kawancen jam'iyyun adawar kasar na CNC wato Coalition Nationale pour le changement ya ce ya janye takara tasa ce domin babu adalci cikin tsarin zaben wanda ya ce kuma ya na cike da kura-kurai.

Wannan dai shi ne dan takarar neman shugabancin kasar na ukku da ya janye takararsa baya ga ministan harakokin wajen kasar Amara Essy da tsohon kakakin majalissar dokokin kasar Mamadou Coulibaly. Yanzu 'yan takara bakwai kenan za su fafata a zaben shugaban kasar ta Cote d'Ivoire na ranar Lahadi mai zuwa ciki har da shugaba mai ci a yanzu Alassane Ouattara.