1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wanzamai sun gina gada a Kaduna

January 23, 2018

Kungiyar wanzamai ta gina wata gada a garin Kwaru da ke Badarawa domin taimakawa al'ummar yankin samun saukin wucewa a sauwwake.

https://p.dw.com/p/2rMae
Überschwemmung in Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Kungiyar wanzaman ta dau matakin gina gadar ne domin rage wahalhalun da al'umma ke fuskanta a kan hanyar, kungiyar ta yi nasarar samun kudin gudanar da ayyukan gina gadar ne ta hanyar yin adashe a tsakanin mambobin kungiyar.

Mal. Mohammadu Wanzam Magajin Askan kawo Kaduna shi ne shugaban kungiyar: " A matsayinmu na wanzaman jihar Kaduna, mun gina gadar ne domin ceto al'ummar da ke yankin, da wadan da ke makotaka da yankin da ke fuskantar cikas a titin."

A baya dai mazauna yankin da ke bi ta gadar na cike da fargaba a duk lokacin da za su wuce ta titin, amma kungiyar wanzaman ta ce ta yi nazarin gyara gadar a matsayin ba da gudumuwar don ci gaban kasa.

Mal. Idi mazaunin yankin Kwaru, ya ce: "Tabbas sauran al'umma sun yaba da yunkurin kungiyar wanzaman na ganin sun gyara gadar da zai taimaki kowa da kowa." Hadaddiyar kungiyar wanzaman reshen jighar Kadunan ta ce irin wannan ayyuka shi suka sa a gaba da nufin taimakawa kasa ta ci gaba.