Warware rikicin Kongo na fuskantar tarnaƙi
November 26, 2012A ƙarshen makon da ya gabata ne shugabanin ƙasashen Yuganda,Kenya, Tanzaniya da na Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo su ka shirya taron ƙoli na mussamman a birnin Kamapla na ƙasar Yuganda, tare da halartar ƙungiyar gamayyar Afrika, inda suka tattana game da halin da ake ciki a rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamnatin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo da 'yan tawayen M23, da suka mamaye birnin Goma da wasu yankunan na gabacin Kongo.
Shugabanin sun ba 'yan tawayen M23 wa'adin kwanaki biyu, domin su fice daga Goma sannan kuma su shiga tattanawa da gwamnatin Kinshasa domin warware rikicin cikin ruwan sanhi.
Yau ne wa'adin ƙarshe da taron shugabanin ya ba 'yan rawaye na ficewa daga Goma: A yau din sun fiddo sanarwa inda suka ba su ga wata takarda ba arubuce daga Kampafa wadda ta bukaci sunjanye daga GOma.
Game da batun tattanawa da gwamnatin Kinshasa kuwa,gwamnatin Joseph Kabila ta ce ba za ta hau tebirin shwara da ƙungiyar M23 ba, sai lokacin da ta fita daga Goma, sharaɗin da shugaban ƙungiyar tawayen M23 Jean-Mari Runiga Lugero ya sa ƙafa ya shure:
"Ba ta kamata janyewa daga birnin Goma ta zama sharaɗin tattanawa tare da mu ba, kamata ta yi a ce ta zama sakamakon shawararin sulhun idan dai da niyar cimma sulhun.Idai aka ce sai mun fita dag Goma, to yaudararmu ce a ke so ayi.Sannan mu fita daga Goma mu tafi ina.?
Jean-Mari Runiga Lugero ya musanta zargin da ake na cewar suna samun ɗaurin gindi daga ƙasar Ruwanda, ya kuma bada dalilan da suka sa ƙungiyar M23 ta shiga gwagwarmaya da gwamnatin Kinshasa:
"Ba da san mune ba mu ka ɗauki makamai, buƙatarmu itace gwamnatin Kongo ta fahinci cewar kasa ta fada cikin matsaloli ta fannoni daban-daban, siyasa tattalin arziki da rayuwar jama'a ta yau da kullum.Sannan mu na so gwamnati ta fahinci cewar burinmu shine warware wannan matsaloli ta hanyar sulhu, saboda haka a shirye mu ke mu hau tebirin shawara da ita, amma ba tare da gitta sharaɗi ba."
A yayin da ake fama da cece-kuce game da tattanawar sulhu jama'a da yaƙin ya rutsa da su na fama cikin uƙuba.Wasu rahotani da ƙungiyar kare haƙƙoƙin bani Adama ta ƙasa da ƙasa wato Human Right Wach da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka gabatar sun zargi 'yan tawayen M23 da gallazawa jama'a a yankunan da suka mamaye, zargin da shugaban ƙungiyar ya musanta:
" Al'ummomin da ke zaune a yankin su da kansu suka ƙaryata wannan rahotani.Sun hito sun shirya zanga-zanga, inda suka danganta rahotani da sharri domin ɓata sunan M23.Rundunoninmu sun ƙunshi sojoji da 'yan sanda masu biyyaya, wanda ke aiki dare da rana, domin kare lafiyar jama'a da dukiyoyinsu".
A yau ma za a cigaba da tattanawa a birnin Kampala na ƙasar Yuganda tsakanin shugaban rundunar ƙasar da na ƙungiyar tawayen M23.sannan a nata gefe itama ƙungiyar Gamayyar Afrika ta kiri taron na musamman a wannan Litinin, game da rikicin Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal