1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu ta lashe kofin zari ruga

November 4, 2019

A wasannin Bundesligar Jamus Bayern Münich ta kori mai horas da 'yan wasanta a yayin da Borussiyoyi ne suka yi kane-kane a saman tebirin gasar.

https://p.dw.com/p/3SR4k
Japan | Südafrika gewinnt die Rugy Weltmeisterschaft gegen England
Hoto: Imago Images/Kyodo News

A wasannin Bundesligar Jamus kuma Yaya babba kungiyar Bayern Münich ce ta kori mai horas da 'yan wasanta a yayin da Borussiyoyi ne suka yi kane-kane a saman tebirin gasar. Muna tafe da karin wasu wasannin da suka hada da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniy ata 'yan kasa da shekaru 17. A wasannin Bundesligar, kasar Jamus kungiyar Bayern Münich ta kori mai horas da 'yan wasanta Niko Kovac bayan wulakancin da ta sha a karshen mako a gaban Kungiyar Frankfurt wacce ta lallasa ta da ci 5-1.

Fussball Bundesliga l  Eintracht Frankfurt vs Bayern München l Lewandowski
Fafatawa tsakanin Frankfurt da Bayern MunichHoto: Getty Images/Bongarts/A. Grimm

Irin yadda aka yi ta yiwa yaya babba ruwan gwala-gwalai a karawar tata da Frankfurt lamarin da a yanzu ya jefa kungiyar a matsayin ta hudu da maki 18 a tebirin na Bundesliga. Tuni ma dai shugaban kungiyar Karl-Heinz Rumminingge ya nada a matsayin kocin wucan gadi na kungiyar Hans Flick mataimakin tsohon mai horas da 'yan wasan kungiyar musamman domin sake kintsa kungiyar a wasannin biyu masu muhimmanci da za ta buga a cikin wannan mako inda a ranar Laraba za ta kara da kungiyar Olympiakos a gasar zakarun Turai, sannan a ranar Asabar mai zuwa ta fuskanci babban wasan kalasiko kasar Jamus da kungiyar Borussiya Dortmund wacce a yanzu ke a matsayin ta biyu da maki 19 bayan da a karshen mako ta casa Wolfsburg da ci 3-0 a filin wasan na Iduna Park. Har yanzu dai Kungiyar Borussiya Mönchengladbach ce ke ci gaba da kasancewa a saman tebirin na Bundesliga bayan da ta je bakunci a Leverkuzen ta kuma daka wa dan gida kashi da ci 2-1.

A sauran wasannin kuma Hoffein Heim ta doke Padarbon da ci 3-0, Bremen da Freiburg sun tashi ba kare bin damo da 2-2. Hertha Berlin ta sha kashi a hannun kanwarta ta Union berlin da ci daya mai ban haushi. Düsseldorf ta doke Kolon da ci 2-0 a yayin da Schalke04 ta je Ausgburg ta kuma doke ta da 3-2.

Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafan amma a wannan Karo a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 da ke gudana a kasar Brazil inda a cigaba da gasar tawagar yan wasan Najeriya Golden Eaglets ta samu hayewa zuwa zagaye na gaba duk da shan kaye da tayi a hannun kasar Australia a wasan karshe na zagayen farko.

1. Bundesliga 10. Spieltag | TSG Hoffenheim vs. SC Paderborn 07
Karawar Hoffenheim da. SC Paderborn Hoto: Imago Images/HMB-Media

Daga batun kwallon kafa bari mu koma na gasar cin kofin kwallon zari-ruga ko rugby ta duniya da ta gudana a kasar Japan, gasar da 'yan wasan Springsboks na Afirka ta Kudu suka lashe kofinta bayan da a wasan karshe da suka kara a ranara Asabar a birnin Yokohama suka lallasa Ingila da ci 32-12. Steven Kitshoff daya daga cikin 'yan wasa farar fata ya bayyana gamsuwar da wannan nasara da suka samu da kuma tasirinta ga kara hada kan 'yan kasar ta Afirka ta Kudu ba tare da banbancin launin fata ba:

"Ya ce nasararmu mai girma ce. Kuma wasan motsa jiki na yin tasiri mai yawa wajen hada kan 'yan kasa baki daya, kuma muna alfahari da farin ciki da haka, ta yadda ta wannan kokari namu muke kokarin kawo sauyin yanayin zamantakewa a cikin kasarmu"

Wannan shi ne karo na uku da Afirka ta kudu ke lashe kofin duniya na kwallon ta zari ruga baya ga wanda ta lashe a shekara ta 1995 da kuma 2007. Kuma kwana daya bayan da Afirka ta kudu ta lashe Kofin duniyan na kwallon Zari Ruga, hukumar kwallon Zari-Ruga ta duniya ta zabi dan wasan na Afirka ta Kudu Pieter-Steph a matsayin dan wasan shekara da ya fi bajinta a duniya kwallon Rugby a yayin da aka zabi shi ma mai horas da 'yan wasan na Afirka ta kudu Rassie Erasmus a matsayin gwarzon shekara na mai horas da yan wasa a duniya Rugby.

A jiya lahadi kenan a gasar Master 1000 ta birnin Paris na aksar Faransa wacce Novak Djokovic dan kasar Sabiya ya lashe bayan da a karawar karshe ya doke Denis Shapovalov dan kasar Kanada da ci 6-3, 6-4.  Kuma a karshen wasan ya bayyana farin cikinsa da nasarar da ya samu yana mai cewa:

Tennis | US Open 2019 | Novak Djokovic
Dan wasan Tennis Novak DjokovicHoto: Reuters/USA Today Sports/R. Deutsch

"Ya ce gasar ta aksance mai muhimmanci gareni domin ban baras da koda wasa daya ba. na yi wasa mai kyau, musamman a wasanni uku na baya. Ana tafiya cikin gasar ina kara samun kuzari wasan nawa na dada kyau"

Wannan shi ne karo na biyar da biyar da Djokovic ke lashe shahararriyar gasar Tennis din ta birnin Paris kuma shi ne karo na 77 da ya ke lashe wata gasar kwallon tennis a tarihin rayuwarsa.

A karshe a gasar gudun kafa mai zurfi ta birnin New York karo na 49 wacce dan kasar Kenya Geoffrey Kamworor dan shekaru 26 ya lashe gasar ta tsawon kilomita 42, da mita 195 a cikin awoyi biyu da minti takwas da sakon 13, a yayin da a bangaren mata ma 'yar kasar Kenyar Joyciline Jepkosgei ta zo ta farko a cikin awoyi biyu da mintuna 22 da kuma sakon 38.