1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Djokovic ya lashe gasar Australian Open

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
January 30, 2023

Bayan lashe gasar Australian Open a karo na 10 a Lahadin karshen mako a birnin Melbourne, Novak Djokovic ya samu damar kamo yawan kambun Grand Slam guda 22 da Rafael Nadal yake rike da su.

https://p.dw.com/p/4Mrlj
Tennis | Australian Open | Novak Djokovic
Novak Djokovic ya zama zakaran gwajin dafi a kwallon TennisHoto: Paul Crock/AFP

Dan kasar Sabiyan mai shekaru 35 a duniya Novak Djokovic ya kai wannan matsayi ne, bayan ya doke dan kasar Girka Stefanos Tsitsipas da ci shida da uku da bakwai da shida da bakwai da hudu da bakwai da shida da kuma bakwai da biyar a wasan karshe. Tuni ma sabon jadawalin 'yan wasan Tennis da aka fitar a wannan Litinin ya sanya Djokovic a matsayin gwani na gwanaye, wato a matsayi na daya yayin da abokin karawarsa Tsitsipas ya ci gaba da zama a matsayi na uku wato a bayan dan kasar Spain Carlos Alcaraz da bai halarci gasar ta Ostireliya ba saboda rauni.

Denmark | Nasara | Kwallon Hannu | Mata
'Yan wasan kwallon hannu na Denmark, sun zama zakara bayan lallasa FaransaHoto: picture alliance / dpa

Denmark ta mamaye kasar Faransa a wasan karshe na cin kofin kwallon hannu na mata na duniya da ci 34 da 29, abin da ya bata damar lashe kofin karo na uku a jere bayan nasarar da suka samu a 2019 da 2021. Hasali ma ita Denmark ta yi nasarar kafa tarihi na kasancewa  kasar farko da ta lashe kofi uku a jere a gasar kwallon hannu ta duniya. Sai dai tawagar Faransa da ta zo a matsayi na biyu ta lashe gasar ta duniya sau shida a tarihinta, lamarin da ya sa ta zama wacce ta fi taka rawar gani a gasar kwallon hannu ta mata ta duniya. A karawar neman matsayi na uku kuwa, Spain ta doke Sweden da ci 39 da 36 kuma ta samu lambar tagulla a karo na uku a tarihinta a wannan gasa baya ga ta 2011 da 2021.

Gabon | Tseren Keke | Tropicale Amissa
A karon farko, kasashen Afirka sun zo na hudu da na biyar a gasar tseren kekeHoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

An kammala tseren hawan keke na kasa da kasa da ake wa lakabi da Tropicale Amissa Bongo a kasar Gabon. Duk da cewa wannan shi ne karo na 16 da gasar ke gudana amma ba dan Afirka ba ne ya lashe tseren, a maimakon haka ma dan tseren Denmark Alexander Salby ne ya zo na daya, yayin da Geoffrey Soupe na Faransa ya zo na biyu. Sai dai abin lura a nan shi ne: A karon farko 'yan tsere hudu daga nahiyar sun kammala a matsayi na uku da na hudu da na biyar a gasar ta Gabon, lamarin da ake dangantawa da alamar ci gaba a tseren keke a nahiyar Afirka.

Aljeriya | Oran | CHAN 2022 | Nijar | MENA | Nasara
Jamhuriyar Nijar za ta fafata da Aljeriya a wasan kusa da na karshe a gasar CHANHoto: Hamza Bouhara/picture alliance

A daidai lokacin da aski ya zo gaban goshi a kokarin da kasashen Afirka ke yi na lashe kofin kwallon kafa na 'yan wasa da ke bugawa a cikin gida da ke gudana a Aljeriya, 'yan wasan MENA na Jamhuriyar Nijar sun bai wa marada kunya ta hanyar lallasa takwarorinsu na Ghana da ci biyu da nema a wasan dab da na kusa da na karshe, yayin da  Madagaska ta shammaci Mozambik da uku da daya. Duk da cewa wannan shi ne karon farko da Tsibirin Madagaska ke halartar wannan gasa, amma tana taka kyakkyawar da ta kai ta ga doke Ghana da Sudan a  wasansu na rukuni. A nata bangaren, Nijar za ta buga wasan kusa da na karshe na farko a tarihin gasar CHAN bayan da ta halarta sau hudu, sakamakon yin waje road ta Kamaru a zagayen farko da ci daya da nema tare da nuna wa Ghana 'yar yatsa. Hasali ma dai Nijar ta nuna karfinta na kare kanta daga abokan hamayya, kuma godiya ta tabbata ga mai horas da 'yan wasa Harouna Doula wanda ya samar wa Nijar duk manyan nasarorin kwallon kafa da ta samu. Mai shekaru 57 a duniyar ne ya kai MENA ga cancantar zuwa gasar CHAN ta 2011 da AFCON ko CAN  a 2012 baya ga lashe gasar yankin UEMOA a 2010 da ya yi. Wannan ne ma ya sa ma'abota kwallon kafa a Nijar suka kara azamar goya wa kungiyarsu baya, a lokacin da MENA ta share musu hawaye na kai wa matsayin kololuwa na CHAN sakamakon doke Ghana da ta yi. Sai dai wasan kusa da na karshe da Aljeriya a birnin Oran zai yi tsauri ga Nijar, saboda mai masaukin bakin ta sha alwashin lashe kofin da ta shirya. Ita kuwa Madagaska za ta kalubalanci Senegal, a wasan na kusa da na karshe.

Bundesliga | Bayer Leverkusen | Borussia Dortmund
Borussia Dortmund ta samu nasara a kan Bayer Leverkusen a karshen makoHoto: Lars Baron/Getty Images

A Jamus kuwa an gudanar da wasannin mako na 18 na Bundesliga a karshen mako, kuma a karo na uku a jere kana a karo na biyu a gida Bayern Munich ta sake yin tuntube, inda ta yi kunnen doki da Eintracht Frankfurt ci daya da daya. Wannan canjaras ya takawa Bayern birki a kokarin da take na sake zama zakara, inda duk da cewa tana saman teburi da maki 37 amma maki daya ne ke tsakaninta da Union Berlin wacce ta doke 'yar uwarta Hertha Berlin da ci biyu da nema. Ita kuwa kungiyar Leipzig tana biye mata baya da maki 35 bayan da ta samu nasara a kan Stuttgart da ci biyu da daya. Hakazalika akwai  wasu kungiyoyi biyu na Jamus da su ma ke hankoran samun wakilci a gasar zakarun Turai wato SC Freiburg, wacce ta lallasa  Augsburg da ci uku da daya da kuma Borussia Dortmund wacce ta doke Bayer Leverkusen da ci biyu da nema. Ko da mai horas da 'yan wasan Dortmund Edin Terzic sai da ya ce kungiyarsa ta fara da kafar dama a wannan shekara ta 2023, ganin cewa tana a matsayi na hudu a saman teburin Bundesliga a yanzu haka. A kasan teburin Bundesliga kuwa, Schalke 04 ta kasance 'yar baya ga dangi da maki 10 kawai bayan da ta tashi babu ci a tsakaninta da Cologne. Wannan yana nufin cewa Hertha Berlin da ke a matsayi na 17 tana gabanta da maki hudu, yayin da Bochum da Stuttgart ke da maki 16 kowannen su.