1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyin arewacin Afirka sun mamaye kofin zakarun Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe MNA
March 9, 2020

Dukkanin kungiyoyi da za su buga wasan kusa da na karshe na kofin zakarun Afirka sun fito ne daga kasashen Maroko da Masar.

https://p.dw.com/p/3Z6hH
Ägypten Fußball Al-Ahly vs Zamalek
Hoto: picture-alliance/Photoshot

A daidai lokacin da aski ya isa gaban goshi a kokarin da kungiyoyi ke yi na neman lashe kofin zakarun kwallon kafa na nahiyar Afirka, Tout Puissant Mazembe ta Kwango Dimukuradiyya ta raba gari da kocinta Pamphile Mihayo Kazembe da mataimakinsa Charles Musonda bayan da aka yi waje road da ita a matakin kusa da kusa da na karshe na wannan gasa. Tuni ma kungiyar ta TP Mazemba ta sanar da Drazen Cvetkovic dan kasar Fararansa da Sabiya mai shekaru 58 a matsayin sabon mai horaswa. Wannan sauyin shugabanci ya zo ne jim kadan bayan da TP Mazembe ta ga samu ta kuma ga rashi, inda ta doke Raja Casablanca a karshen mako ci daya mai ban haushi ba tare da hayewa matakin kusa da na karshe na Champuions lig ba. Dalili kuwa shi ne: yawan kwallaye da kungiyar ta Kwango ta zuwa ba su kai ci biyu da nema da raja ta dokesu a wasan farko ba, ballantana ma ta yi zarra.

Dukkanin kungiyoyi da za su buga wasan kusa da na karshe na kofin zakarun Afirka sun fito ne daga kasashen Maghrib: biyu daga Maroko biyu kuma daga Masar. Zamalek ta Masar ta samu tikitinta na mataki na gaba duk da rashin nasara ci nema da daya a gaban mai rike da kambun Esperance ta Tunisiya, saboda Misirawan sun fara casa takwarorinsu na birnin Tunis da 3-1 a wasan farko. Ita kuwa Al Ahly ta samu damar hayewa matakin kusa da na karshe sakamakon kunnen doki 1-1 da ta yi da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu baya nasarar da ta samu a wasan farko 3-1. Ita da kuwa Wydad Casablanca ta barasa da wasanta a gaban Etoile du Sahel amma bai hana ta zuwa mataki na gaba ba.

Manuel Neuer mai tsaron gidan Bayern Munich bayan da kungiyar ta ci kwallo a wasanta da Augsburg
Manuel Neuer mai tsaron gidan Bayern Munich bayan da kungiyar ta ci kwallo a wasanta da AugsburgHoto: Imago Images/kolbert/B. Schreyer

A nan gida Jamus kuwa, Bayern Munich ta ci gaba da jan zarenta a gasar Bundesliga inda ta ci gaba da zama a saman teburi da maki 55 bayan da ta yi nasara a gaban Augsburg da ci 2-0 a mako na 25. Wannan dai shi ne karo na karo na bakwai cikin wasanni takwas da Yaya-babba ta samu nasara tun bayan fara zagaye na biyu na kakkar 2019-2020. Ita ma Borussia Dortmund ta samu ci gaba a karon batta da ta yi da takwararta Borussia Mönchengladbach inda aka tashi ci biyu da daya, lamarin da ya bai wa yaya-karama damar hayewa mataki na biyu da maki 51. Tuni ma dai kungiyar Gladbach wacce a yanzu ta ke a matsayi na biyar da maki 41 ta fara cire rai da zama gwanar bana, kamar yadda mai horaswarta Marco Rose ya bayyana.

Kungiyar da ita ma ta samu komabaya a wannan mako ita ce RB Leipzig wacce ta tashi wasa da Wolfsburg nema da nema, lamain da ya sata asarar matsayi na biyu zuwa na uku a teburin Bundesliga. Wannan dai shi ne canjaras na biyu a jere da kungiyar da Jilian Nagelsman ke horaswa ta yi, kuma na hudu tun bayan da aka fara zagaye na biyu na wasannin lig din Jamus. Saboda haka ne shi matashin kochin na Leipzig ya nuna bacin ransa dangane da rawar da suka taka.

Amma kuma a nata bangaren kungiyar Leverkusen ta bai wa marada kunya inda ta yi nasarar doke Frankfurt da ci hudu da nema a filin wasaa na BayArena, lamarin da ya bata damar darewa a matsayi na hudu da maki 47.

Matakan kariya daga cutar Coronavirus a filin wasan kwallon kafa
Matakan kariya daga cutar Coronavirus a filin wasan kwallon kafaHoto: picture-alliance/dpa/S. Hoppe

Cutar numfashi ta Coronavirus na ci gaba da barazanar ga harkokin wasanni a kasashe da rukunoni dabam-dabam na duniya. Ko da a nan Jamus, babu tabbas cewa jadawalin gasar Bundesliga zai ci gaba da gudana kamar yadda aka tsara tun da farko. Ministan lafiya na tarayya Jens Spahn ya yi kira a ranar Lahadi da a soke duk taron jama'a da ya kunshi mutane sama da dubu a fadin Jamus ciki har da na kwallon kafa sakamakon yaduwa da cutar ke yi. Duk da cewa ya zuwa yanzu, babu wasan kwallon kafa ko daya da aka dakatar ko aka soke, amma hukumar hada lig din kwallon kafar Jamus (DFL) ta mayar da martani, tana mai cewa ba za ta yarda da jinkarta lokacin karshen kakar wasa ko da rana daya da aka tsara a karshen watan Mayu ba.

A kasar Italiya kuwa, wasannin kwallon kafa na babban lig din kasar ta Serie A na gudana ba tare da halartar 'yan kallo ba. Hukumomin kasar ma sun fara nazarin dakatar da wasanni baki daya sakamakon yaduwar cutar Coronavirus. Ita kuwa Faransa ta sanar cewa wasan zakarun Turai.