Wasu jami'an gwamnatin Najeriya sun mutu a hatsarin jirgin sama
December 16, 2012Talla
Gwamnan jihar kaduna da ke a yankin arewacin Tarrayar Najeriya Patrick Ibrahim Yakowa da tsohon mai bai wa shugaban ƙasar shawara a kan al'amuran tsaro janar Azazi Allah ya yi masu cikawa a wani hatsarin jirgin sama da ya auku.
Hukumomi sun ce mutane a ƙalla guda shidda suka mutu a cikin hatsarin da wani jirgin saman soji mai saukar ungulu ya yi da su a jihar Bayalsa. Shugaban ƙasar ta Najeriya ya ba da ummarnin da a gudanar da binciken gaggawa domin gano dalilan hatsari. Wannan dai shi ne karo kusan na barkatai da ake fama da hatsarin jirgin sama a Najeriyar, wanda a cikin sa a kan samu asaran rayukan jama'a.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman