1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu 'yan ta'adda sun kashe akalla mutane 29 a kasar Sin

March 2, 2014

Kasar Sin wato China na fama da hare-haren ta'addanci wadanda take alakantawa da na 'yan awaren Ouïghours a yankunan da harin ke afkuwa.

https://p.dw.com/p/1BI80
Hoto: Reuters

A cewar hukumomin kasar ta Sin, wannan hari ne na 'yan ta'adda da ke nunin cewa 'yan awaren Ouïghours ne ke neman ta da zaune tsaye a wasu yankunan kasar.

Dama dai cikin 'yan kwanaki da suka gabata ranar buda zaman taron majalisar dokokin kasar ta Sin, wani harin ya yi sanadiyar jikkata mutane 130 a cewar kamfanin dillancin labaran kasar.

Wasu wadanda harin ya rutsa da su, da ma wadanda suka gane ma idanunsu abun da ya wakana, sun ce maharan sun shigo wannan tasha ce, ta Kunming da ke babban birnin yankin Yunnan inda suka yi ta soke masu bulaguro da suka yi layi wajan sayan tikitinsu da wukake.

Akalla dai 'yan sanda sun harbe hudu daga cikin maharan sannan suna cikin neman saura.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal