1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kotu a Chadi na zaman yin shari'a na tsofin jami'an gwamnatin Hissene Habre

Abdourahamane HassaneNovember 14, 2014

Wata kotu a birin Ndjamena na ƙasar Chadi ta soma yin wani zama na musammun a karon farko na sauraron ƙaran wasu mutane guda 29.

https://p.dw.com/p/1DnsH
Hissene Habre
Hoto: picture-alliance/dpa

Ana dai zargin mutanen ne da haɗin baki da tsohon shugaban ƙasar Hissene Habre,wajen aikata kisa da azabtar da jama'a a lokacin mulkinsa daga shekaru 1982 zuwa shekarun 1990.

Daga cikin waɗanda suka gurfana a gaban kotun har'da Mahamat Djibrine tsohon shugaban hukumar bincike na ƙasar da kuma wasu sauran jami'an na hukumar leƙen asiri. Tshohon shugaban na Chadi wanda aka yi wa juyin mulki a shekarun 1990 ana zarginsa da akaita kisan gilLa a kan wasu daruruwan mutane.