1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata kotun kasar Masar ta ba da umarnin sakin Mubarak

August 21, 2013

A ranar Alhamis ake sa ran sakin tsohon shugaban na Masar saboda a cewar lauyansa babu wasu dalilai na ci gaba da tsare Hosnui Mubarak din.

https://p.dw.com/p/19U8u
epa03830622 (FILE) A file photo dated 13 April 2013 shows former Egyptian President Hosni Mubarak (L) on a stretcher looking on from behind the bars of a cage inside the court room during his trial at the Police Academy in Cairo, Egypt. Media reports on 19 August 2013 citing judicial sources and a lawyer of the former president claim that judicial authorities ordered a release of Mubarak from jail and that the former president could be freed during this week. EPA/KHALED ELFIQI *** Local Caption *** 50788437
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata majiyar shari'a da kuma ta jami'an tsaro a kasar Masar sun ce a wannan Laraba wata kotun kasar ta ba da umarni da a sako tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak. Abin nufi yana iya barin gidan kurkuku a ranar Alhamis kamar yadda lauyansa ya nunar inda ya kara da cewa babu wasu dalilai na ci gaba da tsare shi. Mubarak mai shekaru 85 an sake zaman sauraron shari'arsa a kan zargin ba da umarnin kashe masu zanga-zanga lokacin juyin juya halin shekarar 2011 wadda ta kai ga faduwar gwamnatinsa. Sai dai tuni ya kammala zaman wakafi na farkon shari'a kamar yadda aka amince dangane da wannan batu. A bara aka yanke wa Mubarak hukuncin daurin rai da rai don ya gaza hana kisan masu zanga-zanga. Amma a farkon wannan shekara wata kotu ta amince da karar da ya daukaka inda ta ba da umarnin sake sauraron shari'ar. A wani labarin kuma kungiyar EU na duba batun dakatar da hadin kai da Masar. A wannan Laraba ministocin harkokin wajen EU ke tattaunawa a birnin Brussels game da halin da ake ciki a kasar ta Masar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu