Wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka a Najeriya
December 26, 2016Talla
Wani jami'in kungiyar agajin gaggawa ta Nema Ibrahim Abdulkadir ya ce mata biyu ne ke dauke da bam, yayin da daya ta tashi da ita ba cikin shiri ba,ta raunata mutane da dama,kana daya aka kamata kafin ma ta tayar da bam din. Ya kuma ce yanzu haka mutanen da suka jikkata an garzaya da su zuwa asibiti inda ake yi musu magani.