1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Watsi da ƙalubalantar zaɓen Mugabe

August 16, 2013

Jami'yyar MDC mai adawa a Zimbabwe ta ce ta janye ƙarar da ta shigar kotu, wadda ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen Mugabe domin a ganinta Kotun ba za ta yi adalci a shari'ar ba

https://p.dw.com/p/19RHs
Zimbabwe Prime Minister and leader of the opposition Movement for Democratic Change (MDC) Morgan Tsvangirai speaks at a news conference in Harare, June 13, 2013. Tsvangirai on Thursday rejected a plan by President Robert Mugabe to hold an election on July 31, accusing his rival of breaking the constitution and formenting a political crisis in the southern African nation. REUTERS/Philimon Bulawayo (ZIMBABWE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Morgan TsvangiraiHoto: Reuters

Jam'iyyar Movement for Democratic Change MDC a Zimbabwe ta janye ƙarar da ta shigar kotu, inda take ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya mayar da Robert Mugabe kan madafun ikon ƙasar. Jam'iyyar ta MDC ta ce da wuya kotu ta yi mata adalci, ta kuma zargi jami'an zaɓe da ɓoye hujjoji masu muhimmanci.

Mai magana da yawun jam'iyyar Douglas Mwonzora ya faɗaw a manema labarai cewa hukumar zaɓen Zimbabwe ba ta amince ta miƙa duk wasu bayanan da suka shafi zaɓen na watan Yuli ba, abin da ya haɗa da yawan mutanen da suka yi zaɓe, ba tare da sunayensu sun kasance a cikin jerin sunayen waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a.

A nata ɓangaren hukumar zaɓen ta ZEC ta ce ba ta da hurumin miƙa duk waɗannan bayanan ba, domin a cewarta ba su da wata alaƙa da ƙalubalantar zaɓen da jam'iyyar MDC ta yi.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh