1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO na bukatar karin kudade kan yaki da Ebola

January 23, 2015

A kokarin da ta ke na neman kawo karshen cutar Ebola, Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce ta na neman taimakon kudade da karin mutane masu aiki, don ganin hakarta ta cimma ruwa.

https://p.dw.com/p/1EPo8
Hoto: Reuters/Remo Casilli

Hukumar Lafiya ta duniya WHO da ke neman wani sabon taimakon kudade kan yaki da cutar Ebola, ta ce ko da yake an samu karancin masu kamuwa da cuta, amma dai har yanzu da sauran rina a kaba wajan yaki da cutar ta Ebola. Da ya ke magana Bruce Aylward jagoran kula da yaki da cutar ta Ebola a hukumar WHO, ya ce abubuwan da hukumar ke nema su ne kudade, da kuma karin mutane masu aiki, inda ya sanar cewa akalla kudade milian 350 na dallar Amirka ne ake nema don kawo karshen wannan cuta ga baki dayanta.

Wakilin na WHO a yaki da cutar ta Ebola ya kara da cewa ya zuwa tsakiyar watan Febrairu, ganin halin da ake ciki yanzu, zasu fuskanci matsalar kudi ga baki daya, inda ya ke ganin idan dai har a kwai dukkan abubuwan da suka da ce na yaki da wannan cuta, to ana iya kawo karshen ta cikin watanni uku ko hudu masu zuwa. Hukumar ta Lafiya ta kara cewa, har yanzu tana bukatar karin ma'aika a kalla 300 a kasashen na Saliyo, Gini da Laberiya inda wannan cuta tafi kamari.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman