1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta fara amfani da maganin gwajin Ebola

Yusuf BalaJanuary 8, 2015

An kai ga mataki na karshe na fara amfani da magungunan gwaji na allurar Ebola da za ta fara aiki daga wannan Janairu ko Fabrairu a kasashen da cutar tafi kamari.

https://p.dw.com/p/1EHc5
Genf Einlieferung Felix Baez Sarria Ebola Patient 21.11.2014
Hoto: AP Photo/Julien Gregorio, Geneva University Hospital

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa a kokarin da masana harkar hada magunguna suka kammala, a yau Alhamis cikin wannan wata za a fara aiki da allurar gwajin. Idan har aka ga nasarar maganin gwajin maganin zai wadata watanni kadan baya.

Kimanin kwararru 90 ne daga kamfanonin hada magunguna da cibiyoyin lafiya da ma'aikatun lafiya suka hadu a hedikwatar Hukumar ta Lafiya ta Duniya WHO don yin nazari kan maganin gwajin kafin a fara amfani da shi a kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea. Tuni dai wannan cuta ta Ebola ta hallaka sama da mutane dubu takwas a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.