1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar cutar Aids a Jamus

August 10, 2005

Alkaluma sun nuna cewar kimanin mutane dubu 45 ke fama da AIDS/HIV a Jamus yanzu haka

https://p.dw.com/p/BvaZ

A cikin wani binciken da ta gudanar a wajejen karshen shekara ta 2004, wata cibiyar binciken da ake kira Robert-Koch-Insitutut dake nan Jamus ta gano cewar akalla mutane dubu 45 ne ke dauke da kwayoyin cutar Aids a kasar. Kuma ko da yake Jamus ce a matsayi na 14 a tsakanin kasashen Turai dangane da yaduwar kwayoyin cutar ta Aids, kazalika tana da kyakkyawan matsayi a tsakanin sauran kasashe na duniya, amma fa wannan alkaluma da aka bayar, kamar yadda shugabar cibiyar kula da manufofin kiwon lafiya da wayar da kann jama’a ta Jamus Elisabeth Pott ta nunar, abu ne dake yin nuni da yadda kwayoyin cutar ke samun kafar yaduwa a kasar ba kakkautawa. Ta ce a cikin shekarun baya-bayan nan mutane sun yi ko oho da matakan kariya, musamman ma a tsakanin masu shekaru 16 zuwa 44 da haifuwa, wadanda kuma ba su da aure. A yayinda a shekara ta 2003 kimanin kashi 78% na masu irin wannan alaka ke amfani da kwaroron roba, adadin ya ragu zuwa kashi 70% kacal a shekarar da ta gabata. Kuma ko da yake adadin masu kamuwa da kwayar HIV a nan kasar ya gaza mutum dubu biyu a shekara, amma alkaluman da aka bayar sun yi nuni da bunkasar kashi 6% na yawan masu kamuwa da kwayar HIV daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2004, in ji Elisabeth Pott. Duk mai sauraron rahotannin da kafofin yada labarai ke gabatarwa dangane da cutar Aids zai yi zaton cewar wannan wata cuta ce da kawai ta shafi kasashe masu tasowa na Afurka da kudu-maso-gabacin Asiya. Abu mafi a’ala a cewar darektar cibiyar ta kula ta manufofin kiwon lafiya da wayar da kann jama’a ta Jamus, shi ne a ankara da gaskiyar cewa cutar Aids, cuta ce da ta zama ruwan dare a dukkan sassa na duniya sakamakon kusantar da ake dada samu a dangantakar kasa da kasa. Elisabeth Pott ta ce wajibi ne a wayar da kann matasa a game da tahakikanin gaskiyar cewa, har yau fa lalube ake yi a cikin dufu, amma ba a samo takamaiman maganin cutar mai karya garkuwar jikin dan-Adam ba. A yayinda a shekara ta 1987 gwamnati ta ware tsabar kudi na DM miliyan 50 a matakanta na yaki da yaduwar cutar ta Aids, amma a yanzu an wayi gari ana fama da karancin kudi wajen tafiyar da wannan gagarumin shiri, inda yawan abin da gwamnati ke kasaftawa bai zarce Euro miliyan tara ba a shekara, tun abin da ya kama daga shekarar 1998. A sakamakon haka aka samu mummunan koma baya a matakan wayar da kann matasa dangane da barazanar kamuwa da wannan cuta. Wajibi ne a yi taka tsantsan wajen tsumulmular yawan abin da ake kashewa domin wayar da kann jama’a game da cutar ta Aids, saboda murna zata iya komawa ciki idan aka ba da la’akari da yawan abin da za a kashe wajen jiyyar masu cutar wanda zai ninka yawan kudaden da aka yi tsumulmularsu fiye da kima.