Yajin aikin ma'aikata ya gurgunta harkoki a Filato
December 11, 2012Bankuna, gdajen mai, wuraren harkokin jama'a da kuma ofisoshin gwamnatin jiha da na tarayya sun kasance a kulle.
Tun da sanyin safiyar wannan Talata dai shugabannin ƙwadago a jihar Filato suka soma kewayawa zuwa ofisoshin gwamnati daban daban domin tabbatar da ganin cewar sun bi ƙa'idar shiga yajin aikin. A sa'ilin da wakilinmu a Jos Abdullahi Maidawa Kurgwi ya kewaya birnin Jos, ya tarar da 'yan ƙwadagon tare da sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Filato Chris Olakpe a ƙofar shiga sakatariyar gwamnatin jiha, yana roƙon 'yan ƙwadagon cewar ka da yajin aikin ya kai su ga lalata dukiyoyin jama'a.
Garin na Jos na cikin matakan tsaro, haka ma labarin yake a akasarin yankunan ƙananan hukumomin jihar 17, to ko ina wannan yajin aiki ya dosa, komarade Jibrin Bancir, shine shugaban ƙungiyar ƙwadago na jihar Filato yayi ƙarin bayani, inda yace: "sun fara kenan sai duk lokacin da gwamnatin jihar Filato ta biya su kuɗin albashin su na watanni shida."
Haramtaccen yajin aiki
To sai dai kuma gwamnatin jihar ta Filato ta ce wannan yajin aiki ya saɓa ƙa'ida domin kuwa na farko bai kamata ya zama na gama gari ba, hakan nan kotu ta baiwa 'yan ƙwandagon takardar dakatar da su shiga yajin aikin kamar yadda kakakin gwamnatin jiha Yiljab Abraham ya nunar.
To amma kuma shugabanin ƙwadagon suka ce ba su sami wata takarda ba daga kotu, don haka suka tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani. Wasu daga ma'aikatan sun ce wannan shi ne matakin ƙarshe da suka ɗauka na neman hakkin su. Rahotanni daga Shendam, Langtang da wasu yankunan jihar sun ce an rufe hanyoyin mota, shaguna, da ofishoshin gwamnati don nuna biyayya ga wannan umurni da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da bada, da zummar ganin cewar gwamnatin jihar Filato ta bai wa ma'aikatan yankunan hukumomin hakkokin su.
Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Mohammad Nasiru Awal