1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da ci da gumin yara a duniya

February 12, 2013

A daidai lokacin da ake raya ranar yaki da sa yara aikin karfi ciki har da na soja, za a bude shari'ar wata kungiya ta Faransa wacce ta nemi sace wasu yaran Chadi a shekara ta 2007.

https://p.dw.com/p/17cZK
Hoto: picture-alliance/dpa

 A wannan talatar ne a ke saran bude zaman kotu a birnin Paris na Faransa domin ci-gaba da shari'ar wata kungiyar kasar da akewa zargi cin amanar wasu yaran Chadi.
A shekara ta 2007 ne wata kungiya mai rajin kare hakin yara mai sunan Arche de Zoé ta kasar Faransa ta fada cikin wani rikici bayan da jami'an ta suka sace wasu yara 'yan kasar Chadi kimani 103 a matsayin yara marayu. A lokacin kasashen Faransa da Chadi sun saka kafar wando guda bayan da hukumomin N'djamena suka cafke magabatan kungiyar. Sai dai daga bisani shugaban kasar Faransa na wancan lokacin Nicholas Sarkozy ya je kasar ta Chadi takanas domin belin mutanen.

Kasar ta Tchadi ta shigar da kara inda  wata kotu a birnin Paris ta yanke musu hukuncin daurin shekaru a gidan wakafi. Wannan shari'ar na zuwa ne a daidai lokacin da ake bukukuwa ranar yaki da sa yara aiki karfi ciki har da na soja a duniya.Ko da yake shugaban kungiyar Eric Breteau,d a matarsa Emile Lelouche na a kasar Afrika ta kudu, amma kuma bai hana kotun ta yanke hukuncinta a farkon watan Disamban shekarar nan da ta gabata ba.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe