1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da ta'addanci a Beljium

November 23, 2010

Beljium ta kama mutane 15 bisa zargin yunkurin ayyukan ta'addaci a ciki da wayen kasar.

https://p.dw.com/p/QGTx
Cibiyar yada al'adu ta BeljiumHoto: AB Brüssel

Hukumomin Beljium sun yi nasarar cafke wasu mutane 15 da ake zargi da yunkurin kitsa manakisar ta'addaci a kasar. Kakakin kotun kasar ta Beljium ya ce wadannan mutanen da ke da alaka da kungiyoyin da ke da tsattsauran ra'ayin addini, an kamasu ne a kasashen Nertherland, da Jamus da kuma ita kanta Beljium.

Galibin wadanda ke hannu jami'an tsaron na rike ne da passport na kasashen Turai ciki har da ita kanta Beljium da ,Jamus, da Rasha, da kuma Moroko a daya hannu. Daga cikin laifufukan da ake zarginsu da aikatawa, har da hada kai da 'yan tawayen Tchetcheniya, da kuma tallafa wa ayyukan ta'addaci da makudan kudade a wannan kasa, tare da yada manufofin kyamar wadanda ba musulmi ba a kasar Beljium.

Sai dai ministan tsaron Jamus ya bayyana cewa kame-kamen ba su da nasaba da barazanar da kasarsa ke fiskanta ta harin ta'addaci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu