1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

January 13, 2014

Gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta sanar da cewa yakin da ake a kasar ya kawo karshe, bayan da sojoji da 'yan sanda suka koma bakin aikinsu a kasar.

https://p.dw.com/p/1Apj1
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

Kakakin majalisar rikon kwaryar kasar Alexandre-Ferdinand Nguendet ne ya sanar da hakan, inda ya sha alwashin kawo karshen tashin hankalin da ya afku a kasar na tsahon makwanni da ya haddasa asarar rayuka da dama tare kuma da tilastawa dubban 'yan kasar dama 'yan kasashen ketare tsereawa domin tsira da rayukansu.

Kafa gwamnatin ta rikon kwarya dai ya biyo bayan sauka daga kan karagar mulki da shugaban kasar Michel Djotodia ya yi a makon da ya gabata, a wani yunkuri na kawo karshen zubar da jinin da ake fama da shi a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya tun bayan da ya jagoranci 'yan kungiyarsa ta 'yan tawayen Seleka suka kifar da gwamnatin Francois Bozize.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal