1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yamutsi a Bangui lokacin rantsar da Djotodia

August 23, 2013

Watanni biyar bayan karbe ragamar mulki, Michel Djotodia ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kasar da dakarunsa suka daidaita.

https://p.dw.com/p/19VJJ
Former rebel leader Michel Djotodia takes the oath during a swearing-in ceremony on August 18, 2013 in Bangui. Former rebel leader Michel Djotodia was sworn in as president of the Central African Republic on August 18, five months after seizing power in the violence-wracked country. The former French colony's sixth president is tasked with restoring security in the impoverished state and steering the nation through a transition period leading to fresh polls within 18 months. AFP PHOTO/STRINGER (Photo credit should read STR/AFP/Getty Images)
Zentralafrikanische Republik Vereidigung Michel DjotodiaHoto: STR/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda a sharhin da ta rubuta mai taken "An samu shugaban kasa, sai dai babu kasar" jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

"Watanni biyar bayan karbe ragamar mulki, jagoran 'yan tawayen kawancen kungiyar Seleka Michel Djotodia ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda zai ja ragamar shugabancin kasar da dakarunsa suka daidaita. Wannan ma da ya fito fili lokacin shirye-shiryen rantsar da shi. A ranar Asabar lokacin da shugaban Chadi Idriss Deby ya isa Bangui babban birnin Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya ya tarar da wasu a dakin otel da aka tanadar masa. Su kuma sojojin Kongo-Brazzaville sun mamaye harabar otel din don tsaron lafiyar shugaban kasarsu Denis Sasso-Nguesso. Sai da shugaba Djotodia da kansa ya tsoma baki kafin a canja wa Deby masauki. Wata jaridar Chadi ta ce wannan shaida ce dake nuni da tabarbarewar al'amura a Afirka ta Tsakiya tun lokacin da kawance 'yan tawayen Seleka suka hambarar da shugaban mulkin kama karya Francois Bozize a ranar 24 ga watan Maris sannan suka karbi mulki a Bangui."

Binciken cin hanci da rashawa

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta leka kasar Afirka ta Kudu ne inda a ranar Talata wani kwamiti ya fara gudanar da bincike game da zargin cin hanci da rashawa a kasar.

South African President Jacob Zuma arrives ahead of addressing editors at the SA National Editors' Forum (Sanef) in Johannesburg June 24, 2013. South Africans appeared resigned on Monday to the inevitability of one day saying goodbye to former president Nelson Mandela after the 94-year-old anti-apartheid leader's condition in hospital deteriorated to critical.Madiba, as he is affectionately known, is revered among most of South Africa's 53 million people as the architect of the peaceful 1994 transition to multi-racial democracy after three centuries of white domination.REUTERS/Siphiwe Sibeko (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS HEALTH SOCIETY)
Hoto: Reuters

"Wani kwamitin bincike ya fara zaman sauraron ba'asi na wata mummunar hada-hadar cinikin makamai tsakanin Afirka ta Kudu da wasu kamfanonin kera makamai na Turai da ta gudana a cikin shekaru gommai na 1990. Wakilan kamfanonin sun amsa cewa sun ba wa manyan 'yan siyasa toshiyar baki don samun wannan kwantaragi. A 1996 tsohuwar gwamnati karkashin Nelson Mandela ta amince da kudurin samar wa rundunonin mayakan sama da na ruwa makamai masu yawa duk da rashin wata barazana da kasar ke fuskanta daga ketare. Ana nuna shakku game da ko kwamitin zai yi gaskiya domin shugaban kasa Jacob Zuma da wasu jiga-jigan gwamnatin kasar na daga cikin wadanda suka ci gajiyar cinikin makaman."

Tababa game da ikirarin kashe Shekau

Labarin mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram inji jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa a Najeriya ana nuna shakku game da sanarwar nasarar da sojojin kasar suka ce sun samu.

GettyImages 167846563 A poster displayed along the road shows photograph of Imam Abubakar Shekau, leader of the militant Islamist group Boko Haram, declared wanted by the Nigerian military with $320,471 reward for information that could lead to his capture in northeastern Nigeria town of Maiduguri May 1, 2013. Abubakar Shekau, leader of Islamist sect that has killed about 4,000 people since 2009 when it began its campaign of terror is Nigeria's most wanted man, who has been designated a terrorist by the US government. President Goodluck Jonathan has approved the constitution of a Presidential Committee to constructively engage key members of Boko Haram and define a comprehensive and workable framework for resolving the crisis of insecurity in the country. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

"Cikin wani yanayi na rashin tabbas aka samu rahotanni dake cewa wai Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram ya rasu, bayan raunin da ya samu a wata musayar wuta da sojojin Najeriya kusa da kan iyakar kasar da Kamaru a ranar 30 ga watan Yuni, kuma ya cika tsakanin 25 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta. Kasancewa ba tun yau ba rundunar sojan Najeriya ke ba da rahotanni da ba su da sahihanci game da Boko Haram ya sa a wannan karon ma ake saka ayar tambaya game da gaskiyar wannan labari. Hakazalika kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da tabbatar da ikirarin da sojojin suka yi cewa tsauraran matakai da farmakin da suka tsananta kaiwa a kan 'ya'yan Boko Haram tun a cikin watan Mayu sun kai ga hallaka mutum na biyu mafi girma a cikin kungiyar wato Momodu Bama. Hasali ma a ranar 12 ga watan nan na Agusta wato kwanaki 10 ke nan bayan rasuwar da aka ce Shekau yayi, kungiyar ta fito da wani faifayen bidiyo inda aka jiyo shugaban nata na ikirarin hannu a wasu hare-hare da aka kai."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman