1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Cote d'Ivoire sun bukaci a tattauna

Yusuf BalaAugust 31, 2015

Cikin bukatun 'yan adawar dai suna son ganin an rushe hukumar zaben kasar wacce suke ganin tana tare da shugaba Ouattara.

https://p.dw.com/p/1GOjc
Alassane Ouattara, Präsident Elfenbeinküste
Shugaba Alassane Ouattara na Ivory CoastHoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Kawancen adawa a kasar Ivory Coast a ranar Litinin din nan sun bukaci shugaba Alassane Ouattara da ke muradin sake tsayawa takara ya bayyana tanade-tanade da aka tsara a zaben kasar da ke tafe.

A cewar Jean-Jacques Bechio mai magana da yawun kawancen jam'iyyun adawar na NCN ya ce babu yadda za a yi a yi zabe ba tare da zama ba a tattauna kan abubuwan da ake son a cimma.

Wannan kawance na NCN ya hada manyan 'yan siyasa 20 na wannan kasa da suka hadar da tshohon firaminista Charles Konan Banny wanda shi ma ke son tsayawa takara a zaben da kasar za ta yi a ranar 25 ga watan Oktoba.

Cikin bukatun 'yan adawar dai suna son ganin an rushe hukumar zaben kasar wacce suke ganin tana tare da shugaba Ouattara, sannan dukkanin 'yan tawaye da ke dauke da makamai su ajiye makamansu.