1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan adawa a Kenya sun yi iƙirarin yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa

December 29, 2007
https://p.dw.com/p/Chqn

Magoya bayan shugaban ɗan adawa a Kenya Raila Odinga sun yi ikirarin lashe zaben shugaban ƙasar da aka gudana a ranar alhamis. To amma bayan kammala ƙidayar kashi uku cikin hudu na ƙuri´un da aka kada a gundumomi, hukumar zaɓe ta ƙasar ta Kenya ta ce Odinga ke kan gaba da yawan ƙuri´u da ya kai kashi 49 cikin 100 yayin da shugaba mai ci Mwai Kibaki ya ke da kashi 45 cikin 100. Da farko magoya bayan Odinga sun ta da tarzoma don nuna rashin jin dadinsu dangane da jinkirin da ake samu wajen tattara sakamakon zaɓen. Wakilin jam´iyar ´yan adawa ta ODM, William Ruto ya ce dagangan hukumar ke yin haka.