1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Kwango sun yi kashedi ga Kabila

Gazali Abdou Tasawa
September 12, 2018

Wasu manyan 'yan siyasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango su shida da suka hada da 'yan takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa sun gagadi Shugaba Joseph Kabila kan kiyaye dokar tsarin zabe a kasar.

https://p.dw.com/p/34mQx
Kongo Gerard Mulumba und Felix Tshisekedi
Hoto: Imago/Belga

Wasu manyan 'yan siyasar jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango su shida da suka hada da 'yan takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa wato Felix Tchisekedi da kuma Vital Kamerhe sun yi kira ga Shugaba Joseph Kabila kan ya kiyaye dokokin tsarin zabe na kasar domin kauce wa jefa ta a cikin abin da suka kira bala'i, baya ga matsalar talauci da rigingimun siyasar da suka dabaibaye ta. 

Wadannan 'yan siyasa da suka hada da sauran manyan 'yan siyasar kasar da aka haramta wa tsayawa takara a zaben mai zuwa da suka hada Jean Pierre Bemba da kuma Moise Katumbi suka sanya wa hannu sun yi wannan kira ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan Laraba a birnin Brussels.

 'Yan siyasar Kwangon dai sun gitta wasu sharudda tara da suka hada da yin watsi da na'urar zabe ta zamani da kuma tsarkake kundin tsarin zabe da dai sauransu, matakan da suka ce matsawar hukumar zaben ba ta kiyaye su ba, to kuwa ita ke da alhakin duk wani bala'in da ka iya tasowa bayan zabe idan har ya kasance an yi magudi a cikinsa.