1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Siriya sun samu karin agaji

April 21, 2013

Gwamnatin kasar Amirka ta bayyana shirin bai wa 'yan adawar kasar Siriya, taimakon na kwatankwacin kayayyakin da suka kai dala milyan 120.

https://p.dw.com/p/18KBx
Hoto: picture-alliance/dpa

Amirka ta sanar da manufar ta na tallafa wa 'yan adawar kasar Siriya, da kayyakin da suka kai dala milyan 120 wadanda ba su shafi makamai ba. Wadannan kudade za su nunka kudaden da 'yan dawan ke samu na aiyukan jinkai.

Ministocin harkokin waje na kasashe masu neman kawar da gwamnatin kasar, sun gudanar da taro a birnin Istanbul na kasar Turkiya, domin kara matsin lamba ga Shugaba Bashar al-Assad ya ajiye madafun iko. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce babbar manufar ita ce, kawo karshe wahalar da al'ummar Siriya ke fuskanta. Sannan ya kara da cewa mafita guda ita ce ta magance rikicin ta hanyar siyasa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar