1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Siriya sun goyi bayan yaki da Al-Qaida

January 4, 2014

Kawancen masu neman kawo sauyi a Siriya sun kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su taimaka wa 'yan tawaye a fadan da suke yi da 'yan Al-Qaida.

https://p.dw.com/p/1AlLT
Hoto: Guillaume Briquet/AFP/Getty Images

Hadin gwiwar 'yan adawar kasar Siriya na bada cikakken goyon bayansu ga fadan da 'yan tawayan kasar ke gwabzawa da tsoffin aminansu 'yan Jihadi dake da alaka da kungiyar Al-Qaida. Hadin gwiwar 'yan adawar kasar ta Siriya sun yi wannan furci ne cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan Asabar din. A ranar Juma'ar da ta gabata dai aka fara gwabza fadan tsakanin 'yan tawayen da mayaka 'yan Jihadi da su ma ke adawa da gwamnatin ta Siriya, inda hadin gwiwar 'yan adawar ke ganin cewa ya dace mayakan 'yan tawaye su ci gaba da kare akidar sauyi a kasar ta Siriya daga barazanar mayakan sa kai na Bashar Al-Assad da kuma 'yan Al-Qaida da suke kokarin cin amanar akidar sauyin. Tun dai daga birnin Santambul na kasar Turkiya, inda cibiyar su take, 'yan adawar Siriya sun yi kira da kungiyoyin duniya da su gane muhimmancin kawo taimako ga dakarun tawayen masu neman kawo sauyi a fadan da suke tsakanin su da 'yan Al-Qaida.

MawallafI. Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal