1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kai hari a Nairobi

September 21, 2013

Dakarun Kenya sun ce sun tsaurara matakan tsaro a cibiyar kasuwancin birnin da 'yan bindiga suka kai hari har suka hallaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/19lf9
Relatives cry for their loved one as he is brought into hospital after an explosion in Nairobi, Kenya, Friday, Dec. 7, 2012. The Kenyan Red Cross says two people have been killed and eight injured in Friday evening's blast , which was the second in three days. Kenya has seen a series of small-scale explosions over the last year, many from grenades and Kenyan media reported that a member of parliament was wounded in Friday's attack. Kenyan troops moved into Somalia in late 2011, prompting al-Shabab militants in Somalia to vow revenge attacks inside Kenya. Al-Shabab sympathizers are suspected in many of the blast attacks, though authorities have not clearly linked all the attacks to al-Shabab or its sympathizers. (Foto:Sayid Azim/AP/dapd)
Hoto: AP

Dakarun Kenya sun ce sun yi wa 'yan bindigar da suka kai harin a cibiyar kasuwancin da ke a babban birnin ƙasar wato Nairobi ƙawanya, wanda yayi sanadiyyar hallakar aƙalla mutane 30 ciki har da ƙananan yara, ya kuma sanya mutane tserewa domin neman mafaka. An kwashi sao'i da dama ana jin harbin bindiga bayan harin da aka kai tun farko. Jami'an tsaron ƙasar dai sun kewaye babban shagon saida kayayyakin da ake kira ''Westgate Mall'', kuma 'yan sanda da sojoji sun bi kowace ƙusurwar shagon suna neman waɗanda ke da alhakin haddasa wannan ta'asa.

Bisa bayyanan kamfanin dillancin labaran Reuters, wannan harin da aka kai West gate Mall na zaman hari mafi muni tun bayan wanda ƙungiyar Alƙaida ta kai kan ofishin jakadancin Amirkan da ke Nairobi a shekarar 1998 wanda ya kai ga mutuwar mutane fiye da ɗari biyu.

Wasu kafofin yaɗa labaran Kenya sun rawaito cewa an yi garkuwa da wasu mutane amma ya zuwa wannan lokacin babu hujjojin da suka ƙarfafa wannan labari. Dama dai Ƙungiyar Al shabab da ke da mazauninta a Somaliya wadda kuma Kenya ta saba ɗorawa alhakin hare-hare irin wannan ta yi barazanar kai hari a shagon na ''Westgate Mall'' a matsayin martanin sakamakon harin da dakarun Kenya suka kai mata shekaru biyu da suka gabata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane