1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace 'yan Katar 26 a Iraki

Gazali Abdou TasawaDecember 16, 2015

'Yan bindigar sun zo a cikin gwamman motoci da misalin karfe 12 na daren jiya agogon JMT inda suka kutsa a makoncin mutanen da ke a garin Mouthanna kana suka yi awon gaba da su.

https://p.dw.com/p/1HOns
Islamischer Staat Kämpfer Mohammed Emwazi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/SITE Intel Group

Wasu 'yan bindiga sun sace wasu mutane 'yan kasar Katar su 26 a wannan Laraba a birnin Mouthanna na Kudancin kasar Iraki inda suka je farauta.

Wani jami'in 'yan sanda na birnin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa 'yan bindigar sun zo a cikin gwamman motoci masu shiga rayray da misalin karfe 12 na dare agogon JMT inda suka kutsa a makoncin mutanen kana suka yi awon gaba da su.

Wasu jami'an kasar ta Iraki sun ce akwai 'yan gidan sarautar kasar ta Katar daga cikin jerin mutanen da aka sace amma ba a kai ga tantance su ba.

Ministan harakokin wajen kasar ta Katar ya tabbatar da sace mutanen nasu a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce tuni suka fara tattaunawa da hukumomin kasar ta Iraki kan batun hanyar da ya kamata su bi domin ceto mutanen a cikin gaggawa.