1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun halaka mutane a Zamfara

June 4, 2020

Rahotannin da ke fitowa daga arewa maso yammacin Najeriya na nuni da cewa wasu 'yan bindiga sun halaka sama da mutane 20 a kauyukan karamar Hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

https://p.dw.com/p/3dGEk
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da ake zargin maharan sun sato wasu dabbobi, al'umma kuma ta nuna tirjiya. Wani ganau ya shaida wa wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba cewa har yanzu sun kasa rufe gawawwakin jama'a domin da sun je makabarta sai maharan su sake far musu. Kwamishinan tsaro a Jihar Zamfara Abubakar Justice Dauran ya ce gwamnati ta samu labarin wannan al'amari, kuma suna kan hanya zuwa yankin da lamarin ya faru.