1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga suna fadada hare-hare a Najeriya

Amin Suleiman MohammadFebruary 18, 2015

Karuwar hare-haren 'yan bindiga da na kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya na zama babbar barazana ga zabukan kasar

https://p.dw.com/p/1EdsO
Anschlag in Gombe, NIgeria 02.02.2015
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Cikin mako guda hare-haren kunar bakin wake sun hallaka kusan mutane 50 inda ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko haram sun kai hare-hare a garuruwa daban-daban a yankin arewa maso gabashin kasar. Hari mafi muni shi ne wanda aka kai garin Biu inda bayanai daga wasu majiyoyi ciki har da asibiti suka tabbatar da cewa kusan mutane 34 suka mutu wasu da dama kuma suka samu raunika sanadiyyar tagwayen hare-haren kunar bakin wake.

An kuma kai wani harin kunar bakin wake da aka kai garin Potiskum a jihar Yobe inda nan kuma mutane uku ciki har da maharin suka mutu wasu goma sha uku kuma suka jikata.

Boko Haram Flüchtlinge Nigria
Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Akwai kuma hare-haren da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram sun kai Askira inda suka kona gidan sarki da wasu gine-gine na garin sai dai nan ba'a samu alkaluma na yawan wadan abin ya ritsa da suba.

Wannan nan hare-hare wadanda ke zuwa lokacin da ‘yan kasar suka fara lissafin makonni kafin lokacin zabe da hukumomin kasar suka tsawaita sun kasance masu tada hankula tsakanin al'ummar yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ana cikin wannan fargaba ne jagoran Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna, Boko Haram, Abubakar Shekau a fitar da sabon faifayin bidiyo inda ya barazanar cewa ba za su bari a yi zabe ba bayan ya bayyana cewa su ne da alhakin kai hari a garin Gombe.

Sai dai hukumomi na karfafa gwiwar jama'a kan cewa wannan zabe zai gudana kamar yadda aka shirya shi.