1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Chibok na lale da tayin neman sako 'ya'yansu

Al-Amin Suleiman Muhamad/ GATJuly 23, 2015

Shugaba Buhari na Najeriya ya ce a shirye gwamnatinsa take ta tattauna da Kungiyar Boko Haram don sako 'yan matan sama da 200 da aka sace sama da shekara guda ke nan.

https://p.dw.com/p/1G3Ll
Buhari BBOGs
Hoto: Getty Images/Afp/P. Ojisua

A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CNN Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta iya tattaunawa da kungiyar Boko Haram dangane da sakin 'yan matan sakandare na Chibok sama da 200 da kungiyar ta yi garkuwa da su sama da shekara guda.

Sai dai shugaban ya bayyana cewar gwamnatin zata bada damar tattaunawa ne da sahihan ‘yan kungiyar ba wani bangare ba saboda yadda a baya aka samu bangarori da ke ikirarin wakiltar kungiyar inda daga baya kungiyar ke musanta sanin wakilan.

Iyayen yaran na yabawa da shirin

Yawancin iyayen da DW ta tattauna da su sun bayyana fatar ganin an tattauna da kungiyar ko suna da rabon sake ganin ‘ya‘yansu.

Buhari BBOGs
Hoto: Getty Images/Afp/P. Ojisua

Mr Ayuba Alamson daya daga cikin iyayen ‘yan matan da ke zaune a garin Chibok wanda kuma ke gaba cikin masu fafutukar ganin an ceto ‘ya‘yan nasu ya shaida farin cikin da suka ji da jin wannan labari.

"To Allah ya bashi wannan zuciya da duk kasashe da suke mara masa baya don a ga cewar an ceto wadannan yaran. Addu'armu ita ce Allah ya taimakeshi ba wai sai 'yan matanmu na Chibok kadai ba har duk wadanda ke rike a cikin dajin Sambisa, Allah fiddasu lafiya."

Akwai wasu rahotanni da a baya suka nuna cewa an fara irin wannan tattaunawa domin ganin an sako ‘yan matan wanda suke cikin kwanaki akalla 463 bisa sharadin za a saki wasu manyan kwamandojin kungiyar inda ya zuwa yanzu gwamnati da kungiyar ba su gaskata ko karyata tattanawar ba.

Malam Goni Chibok daya daga cikin iyayen ‘yan matan yayi fatan cewa Allah ya sa abin da gaske ne.

"Gaskiya kar abun ya zamo irin na zamanin Goodlock inda aka yi ta zolayarmu ana cewa yau ne gobe ne har aka kwashe sama da shekara. Yanzu muna addu'ar in har da gaske ne Buhari zai iya cetosu, to mun gode kuma Allah ya taimake shi."

Kungiyoyin farar hula na marhabin da matakin

Suma kungiyoyin fararen hula sun bayyana goyon bayansu ga wannan mataki na gwamnatin tarayya da suka bukaci in zai yiwu a fadada tattuanawar wajen ganin 'yan kungiyar sun ajiye makamansu don samar da zaman lafiya mai dorewa.

Nigeria Lagos Demonstration #bringbackourgirls Kampagne
Hoto: Imago/Zuma Press

Abdullahi Muhammad Inuwa wani mai fafutkar kare hakkin bani Adama ne da muhalli a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya ya bayyana gamsuwarsu kan wannan matsayi na gwamnatin Najeriya.

"An yi shekara da shekaru ana ta yaki har yanzu ba abunda aka cimma, har aka zo aka kama wadannan 'yan mata kuma ba a samu wani sakamako ba. Dan haka in har wannan karo abun zai haifar da sakamako mai kyau, abun marahaba ne kuma muna murna. Allah sa a dace."

Batun neman hawa teburin shawara dan magance matsalolin tsaron Najeriya dai na ci gaba da samu goyon bayan masu ruwa da tsaki a harkokin jagoranci inda a ziyarar da Shugaba Buhari ke yi a Amirka ya tatauna da mataimakin shugaban kasar Joe Biben wanda ya bada shawarar cewa amma da karfi kadai ba zai magance matsalar tsaron da kasar ke fuskanta ba.