1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gida daya sun mutu bayan cin guba

August 30, 2022

Al'ummar garin Yabo na jimamin mutuwar wasu mutane 7 'yan gida daya da suka rasu bayan cin abincin da ake zargi da guba a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4GF1C
Kammspinne Bananenspinne
Hoto: picture alliance/dpa/R. Koenig

A Najeriya, al'ummar kauyen Kaurar Yabo da ke cikin karamar hukumar Yabo ta jihar Sakkwato na cikin tashin hankali, bayan da aka samu mutuwar wasu mutane 7 duk 'yan gida guda bayan sun ci wani abinci da ake zargin da guba a wannan Talata.

Yanzu haka mutanen wannan gari na cikin alhini da kuma jimamin wannan lamari da ya faru, ga abin da wani dan uwan wadanda wannan mummunan al'amarin ya faru da su ya shaidawa wakilinmu na jihar Sakkwato Ma'awiyya Abubakar Sadiq....

Wannan na zuwa ne bayan da a Najeriya, rahotanni ke cewa wani ango da 'yan uwansa biyar sun mutu bayan cin abincin biki a jihar Enugu da ke kudancin kasar, ana zargin sun ci guba a abincin.