1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira 47 sun sauka Italiya

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 31, 2019

Jirgin ruwan kungiyar agaji ta Sea-Watch ta Jamus ya isa a wannan Alhamis a birnin Catane na yankin Sicily na kasar Italiya inda ya sauke 'yan gudun hijira 47 da aka ceto kwanaki 13 da suka gabata a gabar ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/3CVlr
Italien Rettungsschiff Sea-Watch 3 in Hafen von Catania eingelaufen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/ANSA/O. Scardino

Kungiyar agaji ta Sea-Watch ta kasar Jamus ta sauke 'yan gudun hijirar da ta ceto duk da barazanar da ministan cikin gidan kasar ta Italiya Matteo Salvini ya yi wa mata na gurfanar da ita a gaban kuliya idan ta kuskura ta shigo da wadannan 'yan gudun hijira. 

An dai karbi 'yan gudun hijirar ne a cikin wasu runfunan tanti wadanda kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta kafa a birnin na Catane. Tun a ranar 19 ga wannan wata na Janeru ne dai wannan jirgin ruwan dauke da 'yan gudun hijira ke yawo a saman teku yana neman samun izinin sauke su a kasar ta Italiya. 

A nan gaba ne dai za a rarraba wadannan 'yan gudun hijira 47 a tsakanin kasashen Turai bakwai na Faransa da Potugal da Jamus da Malta da Luxemburg da Romaniya.