1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gudun hijira na Afirka a Tunisiya.

February 6, 2013

Duban baƙi yan ƙasashen Cadi da Cote d'Ivoire da Najeriya da Nijar da kuma Sudan, waɗanda yaƙin Libiya ya rutsa da su na neman matsayin 'yan gudun hijira a Tunisiya.

https://p.dw.com/p/17ZtZ
Hoto: DW

Kusan mutane dubu biyu ne dai baƙi yan Afirka waɗanda yaƙin Libiya ya tilasa wa ficcewa suka samu mafuka a Tunisiya; waɗanda da farko a ka jigbe su a sansanin yan' gudun hijira na Choucha wanda ke daf da Sahara tsakanin Tunisiya da Libiya.To amma tun daga ƙarshen watan Nuwamba na shekara ta 2012 hukumar yan gudun hijirar ta ce zata tantance waɗanda ya kamata a basu matsayin yan gudun hijirar daga cikin baƙin.

Wahalolin da yan gudun hijirar ke fuskanta .

Khadija yar shekaru kimani 48 yar ƙasar Cadi ce, kuma ta na da ya'ya guda fuɗu ta na kuma cikin tarin jama'ar da suka je suka yi dandazo a gaban ginin hukumar yan gudun hijira na MDD.Ta ce ''ni ban tambayi abinci ba; ko ruwa ;ko kudi ; abinda na ke so shi ne su baiwa yarana kariya''.Khadija ta kwashe kusan shekaru biyu ta na yin buɗa a Libiya inda ta samu aiki ta na yin rayuwarta da yaranta kafin al' amura su burkuce, Saboda yaƙin da ya sa suka bar ƙasar. A yau ta fidda ran samu wannan matsayi daga hukumar.Frederic Tadie ɗan ƙasar Cote d'Ivoire shi ma lamarin ya shafe shi.Ya ce'' wannan dalili shi ne ya sa muga yi banga banga a cikin sansanin ya ce mu ba mu iya komawa Libiya sannan ba zamu iya tsayawa ba Tunisiya ba ;ya ce kana ba zamu iya komawa gida ba ,ya ce wannan ita ce babbar maganar a yanzu hukumar yan gudun hijirar ta yi watsi da mu. To ina zamu.''

Subject: African refugees in Tunisian-Libyan border.   Date: August 2011   Place:Rass Jdir   Photographer:Khedir Mabrouka  Die Bilder hat unser Korri in Tunesien Khedir Mabrouka gemacht. DW hat deshalb die Rechte. Zulieferer: Emad Ghanim
Hoto: DW

Yan gudun hijirar sun rasa wurin zuwa.

Libiya dai sannin kowa ne a yanzu wuri ne da ke tattare da hatsari ga baƙar fata saboda zargin da aka yi ta yi masu cewar sun ba da goyon baya ga mariganyi Gaddafi, Tunisiya kuma bata da wuraran karɓar baƙi.Wannan kuma shi ne gaba kura baya siyaki ga waɗannan mutane da yawancin su ke yin bara domin cin abinci. Othaman ɗan ƙasar Sudan ne ya kuma zo ne daga Darfur. Ya ce ''mun yi gudu daga Libiya sun karɓemu sun samu cikin tantuna kusan shekaru biyu muna zaune; a yanzu sun zo sun ce mana ba zasu ci gaba da amince wa da mu ba ,ba mu san dalili bai.'' Ƙungiyoyin masu fafutuka na ta ƙoƙarin kutsawa domin ganin hukumar yan gudun hijira ta MDD ta taimaka ,amma hukumar tace ta yi iya bakin kokarinta.Nan gaba ne dai a cikin watan Yuni na wannan shekara za a rufe sansanin na yan gudun hijrar na Choucha. Kuma da sannun a hankali mutane na watsewa; da dama daga cikin yan gudun hijirar wasu sun samu sun tafi Amurka.

Subject: refugees in Tunisian-Libyan border:African refugee in Rass Jdir    Date: August 2011   Place:Rass Jdir   Photographer:Khedir Mabrouka  Die Bilder hat unser Korri in Tunesien Khedir Mabrouka gemacht. DW hat deshalb die Rechte. Zulieferer: Emad Ghanim
Hoto: DW

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu