1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na bukatar tallafi EU

Pinado Abdu WabaApril 16, 2015

Gwamnatin Italiya ta bukaci karin tallafi daga Kungiyar EU, sakamakon hatsarin jirgin ruwan da ya afku kwanannan kusa da gaban ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/1F9U0
Italien Corigliano Mittelmeer Gerettete Bootsflüchtlinge Ankunft Hafen
Hoto: picture-alliance/epa/F. Arena

Ministan harkokin wajen Italiyan Paolo Gentiloni ya ce kama daga aikin sintiri da aiyyukan ceto na kan tekun, kashi 90 cikin 100 ya rataya ne a wuyar 'yan Italiya. Gentiloni ya kuma kara da cewa wajibi ne Turai ta taka rawar gani a kasashen 'yan gudun hijirar na asali, ta yadda za su daina sa rayukansu cikin hadari.

A watan Oktoban bara ne Kungiyar ta EU ta kawo karshen aiyyukan jami'an Italiyan dake tabbatar da tsaro kan ruwayen na Turai, wadanda aka fi sani da Mare Nostrum, ta kuma maye gurbinsu da wata mai suna Triton wadanda suke karkashin jagorancin hukumar da ke kula da iyakokin Turai wato Frontex.

Sai dai ita wannan sabuwar ta Triton ta fi mayar da hankali ne kan tsaron iyakokin Turai, fiye da ceto masu gudun hijirar dake tudadowa a jiragen ruwa, a yawancin lokuta tsaffi ko kuma marasa karko.