1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Houthi sun saki firaministan Yemen

Ahmed SalisuMarch 16, 2015

'Yan kungiyar nan ta Houthi da ke rike da babban birnin kasar Yemen sun saki firaministan kasar Khalid Bahah bayan da suka shafe watanni biyu su na tsare da shi.

https://p.dw.com/p/1ErVj
Jemen Regierungschef Khaled Bahah ARCHIVBILD
Hoto: Reuters/Khaled Abdullah

Firaministan Yemen da ya aje aiki a watan Janairun da ya gabata Khalid Bahah ya ce zai fice da babban birnin kasar Sana'a bayan da mayakan Houthi suka sallame shi daga inda suke tsare da shi tsawon watanni biyun da suka gabata.

A wani sako da ya sanya a shafinsa na Facebook, Mr. Bahah ya ce nan gaba kadan ya ke sa ran 'yan Houthi din za su sako wasu daga cikin mambobin gwamnatinsa da su ma suke tsare da su.

Nan ba da dadewa ba ne ake sa ran Bahah din zai tafi birnin Aden inda shugaba Abedrabbo Mansour Hadi ke gudanar da harkokinsa na mulki bayan da tsere daga Sana'a a watan jiya sai dai rahotanni na cewar zai wuce kauyensu na Hadramawt ne don gana da iyalinsa da sauran dangi.

Shugaba Mansur Hadi dai ya bukaci firaministan nasa da ministocinsa da su koma Aden din baki daya don cigaba da aiyyukansu kamar yadda suke yi a baya sai dai ya zuwa yanzu ba a tantance ko za su koma din ba.