1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida 70 sun rasu a 2013 da ke karewa

December 30, 2013

Kimanin 'yan jarida saba'in ne suka rasu yayin da suke bakin aiki musammam ma a wuraren da ake yaki a wannan shekarar ta 2013 da muke shirin bankwana da ita.

https://p.dw.com/p/1AjFY
Motar 'yan jarida da aka yi wa raga-raga da harsashi a fagen famaHoto: picture alliance/dpa

Daga cikin wadannan 'yan jarida saba'in, 29 sun rasu yayin da suke aikinsu na farautar labarai a kasar Siriya wadda ke fama da yakkin basasa, inda karin wasu goma suka mutu a kasar Iraki wadda ita ma ke fama da tashin hankali na masu tada kayar baya.

A kasar Masar ma dai an samu asarar rayukan manema labarai guda shidda musamman ma ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata lokacin da jami'an tsaron kasar suka afkawa masu adawa da juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban kasar Muhammad Mursi.

Tuni dai kungiyoyin da ke kare hakkin 'yan jarida na kasa da kasa suka fara kiraye-kiraye ga kasashen duniya da su sanya idanu wajen ganin an kare rayukan 'yan jarida daga salwanta musamman ma dai a fagen fama kamar yadda aka gani a Siriya da Iraki da Masar da ma kasar Mali inda nan ma wasu 'yan jarida biyu suka rasu bayan da suka shafe kawanki a hannun wanda suka sace su.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal