1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jaridun Turkiyya sun yi watsi da zargin ta'addanci

Abdul-raheem Hassan MNA
July 24, 2017

Ma'aikatan jaridar Cumhuriyet 17 da aka gurfanar a kotu, sun yi watsi da zargin ta'addanci da ake alakanta su da shi. A ranar Litinin din nan ce aka bude shari'ar bayan tsare su a watan Oktoban shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/2h4lR
Türkei Cumhuriyet Journalists In Terror Trial - Istanbul
Hoto: picture alliance/dpa/abaca/C. Erok

Da dama daga cikin 'yan jaridun sun shafe kusan sama da watanni takwas a tsare ba tare da gurfanar da su a gaban kuliya ba. Tun bayan yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Racep Tayyip Erdogan da bai yi nasara ba a shekara ta 2016, 'yan jaridu da dama na cikin takunkumin rashin samun damar gudanar da aiki a fadin kasar.

'Yan jaridu a Turkiyya dai sun gudanar da ranar 'yancin 'yan jaridu ne a lokacin da ma'aikatan jaridar da ke adawa da gwamnatin kasar 17 ke gaban alkali. Idan dai gwamnatin na Turkiyya ta yi nasarar cimma wannan kara, 'yan jaridun za su kasasnce a gidan sarka na kusan sama da shekaru 43. To sai dai irin wannan mataki da Turkiyya ke dauka a kan 'yan jaridu, na ci gaba da ja mata karan tsana daga sauran kasashe mambobin kungiyar Tayayyar Turai da ke kafa hujja da yunkurin take 'yancin fadin albarkacin baki.