1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Kenya na hankoron samun canjin gwamnati

Mohammad Nasiru Awal AS
August 7, 2017

Wasu daga cikin 'yan Kenya na nuna rashin gamsuwarsu da mulkin gwamnatin da ke ci, suna zarginta da rashin cika alkawari.

https://p.dw.com/p/2hpKi
Shugaba Uhuru Kenyatta da dan adawa Raila Odinga
Shugaba Uhuru Kenyatta da dan adawa Raila Odinga

A daidai lokacin da aski ya kai gaban goshi dangane da zaben kasar Kenya inda ake kankankan tsakanin 'yan takarar neman shugabancin kasar, 'yan kasar ta Kenya da za su jefa kuri'a a zaben na ranar Talata, suna fatan samun canjin gwamnati.

Kafin su iya kada kuri'a dole sai wasu 'yan kasar sun je yankunan da suka yi rajista. Wasu sun damu cewa tashin hankali ka iya barkewa a lokacin zaben suna masu yin tuni da rikicin da ya faru bayan zaben 2007.

Wasu daga cikin 'yan kasar na nuna rashin gamsuwarsu da mulkin gwamnatin da ke ci, kamar yadda wannan mutumin mazaunin birnin Nairobi ya nunar.

"Muna sa ran samun canjin da muke bukata. Komai ya yi tsada, rayuwa ta yi wahala. Sun kasa cika alkawuran da suka dauka. Saboda haka muna bukatar canji, muna bukatar sabbin jini wadanda za su ba mu sabuwar alkibla, amma ba irin wadda muke kanta ba yanzu."

Hasashe dai na nuni da cewa ana kankanta tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da babban abokin adawa Raila Odinga.