1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Mali na jiran sabuwar gwamnati

December 12, 2012

Saban Firamiyan Mali Diango Cissoko na shirin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

https://p.dw.com/p/170oP
Dioncounda Traore (C) arrives at the main airport in the capital Bamako, July 27, 2012. Mali's interim president returned on Friday from weeks convalescing abroad after he was beaten up by a mob, facing pressure to form a new government and authorise a foreign military intervention against rebels in the north. Mali needs outside support to recover from twin crises sparked by a March coup in the capital that precipitated the rebel takeover of its northern zones, occupied by Islamists dominated by al Qaeda's North African wing, AQIM. Picture taken July 27, 2012. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)
Dionconda Traore da DiarraHoto: Reuters

Kasa ga sa'o'i 24 bayan murabus ɗin tsafan Firaministan Mali, shugaban riƙwan ƙwarya Professa Dioucounda Traoré ya naɗa Diango Cissoko a matsayin saban Firaminista.

A yayin da al'umar Mali ke cikin jiran sabuwar gwamnati,jama'a na ci gaba da maida martani game da halin da ƙasar ta shiga.

Jim ɗan bayan naɗa shi a matsayin saban Firaministan Mali,Diango Cissoko mai shekaru 62 a duniya ya baiyana mahimman bururukan da ya ke buƙatar cimma, wato ƙwato yankin arewacin ƙasar dake cikin hannun 'yan tawaye da ƙungiyoyin kishin addini Islama,sai kuma shirya zaɓɓuɓuka.Kamin ya hau wannan muƙami Cissoko na matsayin babban mai shiga tsakani na ƙasa.Saidai duk da kyakkyawar shaida da ya samu daga al'umar ƙasa,jama'a sun yi imanin cewar ya na da jan aiki a gabansa saboda dalilai masu yawa.

Shugaban ƙasar Burkina Faso wanda ƙungiyar ECOWAS ta ɗorawa yaunin shiga tsakanin rikicin ƙasar Mali, ya baiyana wasu daga wannan dalilai:

In this still frame made from video provided by ORTM Mali TV, Mali's Prime Minister Cheikh Modibo Diarra resigns during a broadcast on state television from Bamako, Mali on Tuesday, Dec. 11, 2012, hours after soldiers who led a recent coup burst into his home and arrested him. (Foto:ORTM Mali TV/AP/dapd) MALI ACCESS OUT
Modibbo Diarra mai murabusHoto: AP

"Idan kuna tune na sha fadi ina nanatawa, na sha jawo hankali duniya bisa rashin tsarin da rashin tsinkaye da ake tafe da shi a harkokin zartsawar riƙwan ƙwarya ƙasar Mali.Wannan abu da ya faru bai bani mamaki ba kuma cemma na san a rina.Sai dai fatanmu shine ba tare da ɓata lokaci a girka sabuwar gwamnati, wadda za ta duƙufa wajen fidda surfe daga ruwa, ta hanyar tattanawa ta zahiri tsakanin al'umar ƙasar Mali da duk wani ɓangare da ka iya bada gudunmuwa domin cimma burin da aka sa gaba."

Shugaba Blaise Compaore ya baiyana rashin gamsuwa game da yadda sojoji ke yin katsalandan cikin harkokin siyasar Mali, sannan ya zargi shugaban riƙwan ƙwarya Pr.Dioucounda Traoré da nuna sanhin hali:

"A ganina tun da tashin farko Pr. Dioucounda ya nuna sakaci, kamata tayi ya jajurce ya nuna shine shugaban ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.Amma sai yayi kwance da kaya,saboda haka, sai wasu suka yi amfani da wannan dama, domin shisshigi cikin harkokin mulki, har suka wuce makaɗi da rawa.Shi ya sa sojoji suka aikata abinda ya faru ga Firaministan da yayi murabus.

Ya zama wajibi a ƙasar Mali ayi aiki sau da ƙafa da kundin tsarin mulki.Akwai shugaban ƙasa na riƙwon ƙwarya, shine ta kamata ace shine riƙe da zahirin mulki saɓanin al'amarin dake faruwa yanzu."

Gamayyar ƙasa da ƙasa, hasali ma Majalisar Dinkin Duniya, ƙungiyar Tarayya Afrika da ƙungiyar ECOWAS, sun yi tir da Allah wadai ga yadda sojoji suka tursasawa Cheik Modibbo Diarra yin murabus.

Sun yi kira da babbar ga murya ga sojojin ƙasar Mali su koma bariki, su shafawa 'yan siyasa lafiya su gudanar da harkokin mulki.

Links: Coup leader Captain Amadou Sanogo attends a ceremony as former parliament speaker Dioncounda Traore (unseen) is sworn in as Mali's interim president in the captial Bamako, April 12, 2012. Traore took over as Mali's interim president on Thursday from the leaders of last month's coup, promising to hold elections and fight Tuareg and Islamist rebels occupying half the country. Traore, 70, a labour activist turned politician, was sworn in by Supreme Court President Nouhoum Tapily in the capital Bamako as part of a deal to restore civilian rule after army officers staged a March 22 coup in the West African state. REUTERS/Malin Palm (MALI - Tags: POLITICS MILITARY PROFILE) Rechts: Mali's interim President Dioncounda Traore speaks during a news conference at the presidential palace in Abidjan May 16, 2012. REUTERS/Luc Gnago (IVORY COAST - Tags: POLITICS HEADSHOT)
Sanogo da TraoreHoto: Reuters

A halin yanzu dai saban Firaministan ya fara tattanawa da ɓangarori daban-daban domin girka gwamnatin haɗin kan ƙasa.

A halin dake ci dai, ga alamu al'umar ƙasar Mali na cikin jiran sabuwar gwamnati,Oumou Touré Traoré itace shugaba haɗin gwiwar ƙungiyoyin mata na ƙasar,ta baiyana buƙatarsu ga wannan gwamnati:

"Muna jiran abu da yawa daga wannan gwamnati, domin a halin da ke ciki ƙasa ta faɗa cikin mawuyacin hali.Saidai muna kira ga saban Firaminista kar ya manta da mata, domin a domin akwai buƙatar gami karfi a cikin wannan marra".

Kamin ma ya ke kafa gwamnati Diango Cissoko yayi kira ga y'an ƙasar Mali su bashi haɗin kai domin taimaka masa ya fuskanci manyan ƙalubalen da ƙasa ke fama a ciki.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani