'Yan PDP sun yi zanga-zanga a Sokoto

'Yan jam'iyyar PDP a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a bakin ofishin hukumar zaben jihar inda suka bukaci da a bayyana sakamakon zaben gwamna.

Zanga-zangar ta biyo bayan sanarwar da hukumar zaben kasar ta yi cewar zaben jihar bai kammala kasancewar an soke zabuka a mazabu 139 na jihar saboda dalilai daban-daban.

Takara a zaben na Sokoto dai ta fi zafi tsakanin Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP da ke neman wa'adi na biyu da kuma Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Rahotanni masu dangantaka