1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na artabu da masu bore a Iran

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 13, 2022

Jami'n tsaro a Iran na ci gaba da dauki ba dadi da masu boren kin jinin gwamnati a sakamakon mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun 'yan sandan da'a a tsakiyar watan Satumba.

https://p.dw.com/p/4I76I
Masu boren kin jinin gwamnati na kone-kone kan tituna a birnin Teheran
Masu boren kin jinin gwamnati na kone-kone kan tituna a birnin TeheranHoto: AFP/Getty Images

Jami'an tsaro sun yi amfani barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu boren kin jinin gwamnati a Jamhuriyar Muslunci ta Iran. Tuni wasu manyan kasashen ciki har da Faransa suka fara nuna adawarsu da matakin amfani da karfin tuwo don murkushe mata masu zanga-zanga.

Bayan Amirka da Kanada, kasashe membobin Kungiyar Tarayyar Turai sun yi na'am da duk wasu matakan ladabtarwa da kungiyar ke shirin dauka a kan hukumomin Iran da ke hankorin murkushe masu boren.

Fiye da mutane 100 ne suka halaka ciki har da kananan yara a cewar kungiyoyin kare hakin bani Adama a kasar ta Iran, tun bayan barkear zanga-zangar kin amincewa da mutuwar matashiya Amini a tsakiyar watan Satumba.