1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan sanda na ci gaba da gallazawa jama'a a Masar

February 20, 2013

Tun daga makonnin baya ake samun rahotanni na karuwar rashin imanin yan sanda kan masu zanga-zanga da yan adawa a Masar

https://p.dw.com/p/17hsZ
Hoto: Getty Images

Ba wani boyayyen abu bane cewar jami'an tsaro a Masar basa nuna wani sassauci ko imani kan duk masu adawa da gwamnatin wannan kasa. To amma tun daga makonnin baya ake samun karuwar wadanda yan sandan kasar suke ganawa azaba ko cin mutuncinsu ta wasu hanyoyi. Yanayin aikin yan sandan da sauran jami'an tsaron Masar bai canza ba, shekaru biyu bayan kawar da mulkin kama karya na Hosni Mubarak, kamar yadda Farida Makar, ta cibiyar kare hakkin yan Adam dake birnin Al'kahira ta nunar.

Farida Makal tace yan sandan na Masar suna ci gaba da azabtar da jama'a, suna kuma amfani da rashin imani mai tsanani kan yan zanga-zanga, inda a yanzu din ma, kamar dai a zamanin mulkin shugaba Hosni Mubarak, yan sandan suna ci gaba da gwadawa al'ummar Masar karfi fiye da kima. Wani mutum mai suna Hamada Saber yaji a jikinsa game da wannan rashin imani na jami'an tsaro. Lokacin wata zanga-zanga ta adawa da shugaba Mohammed Mursi a gaban fadarsa, yan sanda sun yi masa mummunan duka, bayan da tun farko suka tube shi tsirara. Daga karshe suka rika jansa babu komai a jikinsa kan titi kafin su jefa shi a motar yan sanda su tafi dashi. Farida Makar tace irin wannan abu ya zama ruwan dare a Masar. Yan sandan tun a zamanin mulkin Mubarak, sun saba tube yan zanga-zanga su yi masu duka su jasu kan titi tsirara kafin su kaisu wurin tambayoyi.

Abin da yafi muni game da abin da ya sami Hamada Saber shine, an yi masa duka ne gaban dubban jama'a maimakon kamar yadda yan sandan wani lokaci sukan yi, su kai mutum ofishinsu tukuna kafin su ci mutuncinsa. Ko da shike daga baya Saber yace ba yan sandan ne suka doke shi ba, amma Farida Makar tayi imanin cewar jami'an tsaron ne suka tilasta masa fadin haka, inda sai da iyalinsa suka matsa masa lamba ne sa'annan ya yarda da cewar yan sandan ne suka ci mutuncinsa. Ba kuma abin mamaki bane ganin cewar idan ma mutum ya kai yan sandan kara saboda azabtarwa ko laifin rashin imani, wanda ya kai karar yakan sanya kafar wando daya da yan sandan. Farida Makar tace:

Kairo Anti Mursi Proteste
Zanga-zangar adawa da shugaba Mohammed Mursi a AlkahiraHoto: Reuters

"Bisa al'ada sukan yiwa wanda ya kai karar barazana, ko dai su jefa shi ko iyalinsa gidan kaso, ko su boye wasu abubuwa dake iya zama laifi, kamar kwayoyi ko miyagun magunguna a gida ko a motar mutum. A takaice dai, sun san yadda zasu tsorata mutum, su sanya shi cikin zaman juyayi."

Hamada Saber ba shi kadai ne irin wannan rashin imani ya shafa ba. A bisa rahoton wata kungiya ta kare hakkin yan Adam a Masar, tun daga ranar 25 ga watan Janairu na wannan shekara, yan zanga-zanga akalla dari biyu ne aka jefa su gidan kaso. Wasu daga cikin su yara ne kanana, wadanda aka rika yi masu duka ana azabtar dasu. Wannan abu kuwa, inji kungiyar, musamman yafi tsanani kan yara ne da suka rasa iyayensu, wadanda basu da mai kare su.

Ibrahim, dan shekaru 26, wanda a bara shima aka gallaza masa azaba, yace yana da ra'ayinsa a game da dalilin da ya sanya ake samun rashin imanin jami'an tsaron Masar ko wane lokaci. Dalilin hakan inji shi, yana tattare da tsarin horad da jami'an tsaron ne. Lokacin samun horo, shugabannin yan sandan sukan yiwa kurata duka su rika kaskantar dasu. Idan suka fito sukan dauki fansa na abin da akai masu a makarantun yan sandan.

Mursi in Berlin 30.01.2013
Shugaban Masar, Mohammed MursiHoto: Getty Images

Ko da shike abu mai muhimanci shine yiwa tsarin aiyukan yan sandan na Masar gyara, amma hakan ba zai samu ba, domin kuwa jami'an tsaro sun zama yan amshin shatan masu mulki, wadanda ake amfani dasu domin danne abokan adawa. Saboda haka ne Farida Makar tace bata yi imanin za'a yiwa tsarin aiyukan yan sandan gyara yadda zasu zama masu tabbatar da tsaro da kare hakkin al'umma ba.

Mawallafi: Matthias Sailer/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal